Home / Labarai / Da Kazo Harabar  Gidan Marigayi Balarabe Musa Ma Wa’azi Ne Mai Fadakarwa

Da Kazo Harabar  Gidan Marigayi Balarabe Musa Ma Wa’azi Ne Mai Fadakarwa

 Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana rayuwar marigayi Abdulkadir Balarabe Musa a matsayin rayuwa mai cike da abin ko yi.
Tambuwal ya ce hakika duk wani shugaban siyasa da mai mulki ya tabbatar da yin ko yi da irin yadda marigayin ya yi rayuwarsa mai cike da son kasa tare da jama’arta baki daya.
Gwamna Tambuwal ya ce yazo wannan gaisuwar Ta’aziyya ne a madadin shi kansa,iyalansa da al’ummar Jihar Sakkwato baki daya.
Tambuwal wanda yazo Kaduna har gidan marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa domin yi wa iyalin marigayin ta’aziyyar rasuwarsa “da kazo cikin wannan gidan na marigayi kasan akwai abin wa’azi da fadakarwa tare da samun abin ko yi a cikin gidan, don haka idan ana son ayi gadonsa to ayi ko yi da shi tukuna”.
“Naso in zo tun lokacin da aka yi wannan rasuwar amma saboda dai haka Allah yaso shi yasa sai a wannan lokacin na samu zuwa”.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ci gaba da cewa ” hakika ya samu darussa da dama a lokacin rayuwar marigayin , saboda ina zuwa ko in kira marigayin a waya domin mu yi maganganu na neman shawara musamman lokacin da nake shugaban majalisar wakilai ta tarayya na karu da shawarwari sosai”. Inji Tambuwal.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya halarci gidan marigayin tare da tawagarsa da kuma manya manyan Jiga Jigan Gwamnati karkashin jam’iyyar PDP da suka hada da Injiniya Bello Suleiman da Musa Dan Iya da dai sauransu duk sun yi gaisuwar ta’aziyyar ne a madadi jama’ar Jihar Sakkwato baki daya.
Babban dan marigayin Dokta Ibrahim Balarabe Musa ya yi godiya da Gwamnan da sauran jama’ar da suka halarci gaisuwar mahaifin nasu.
Inda ya ce hakika jama’ar duniya da dama sun amfana da rayuwar marigayin ta fannin shawarwari da kuma tsarin shugabanci da fannoni da dama da ba su misaltuwa.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.