Bashir Bello, Daga Majalisa Abuja
Sanata Muhammadu Adamu Aleiro dan Majalisar Dattawa mai Wakiltar Kebbi ta tsakiya ya ce dalilin su na son ganin Shugaban Kasa Bola Tinubu shi ne domin su tabbatar da cewa rahotanni da aka rubuta a baya tun shekara ta 2015 zuwa yanzu, wadanda suka bayar da shawarwari na yadda za a magance matsalar tsaro an yi amfani da su.
“Daukacin yan majalisar Dattawan Najeriya ne ke bukatar Suga shugaban kasa ido da ido domin tattauna batutuwan halin da Najeriya ke ciki da kuma tattauna wadansu batutuwan da ke cikin wani rahoton da aka rubuta tun a can baya”, inji rahoton.
Sanata Adamu Aliero, ya ce sun dauki wannan matakin ne domin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi Kasar nan.
Ya ce Majalisar Taraiya ta baiwa Jami’an tsaro wadatattun kudade a kasafin kudi da aka gudanar a Majalisa ta Tara da ta Goma amma hakan bai sa an sami wani canji na kuzo mu gani ba.
Sanata Aleiro ya kara da cewa a kwanakin baya Majalisar Dattawa ta gaiyaci Hafsoshin Sojan Kasar da duk masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro kuma sun tattauna a kan batutuwa da dama amma duk da haka ba a jima ba sai da aka kashe sama da mutum 50 a Jihar Benue, wanda hakan abin bakin ciki ne kwarai.
Saboda haka, ba za su zura ido kawai su na ganin ana ta kashe yan Najeriya babu gaira babu dalili ba.
Ya ce “dole a dauki mataki ko a cire Hafsoshin tsaron idan ba za su iya ba a canza su da wadanda za su iya ko kuma ayi duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen wannan matsala a Kasa baki daya”.
A wani bangaren kuma Sanata Aleiro ya ce baya goyon bayan amfani da ake yi da yan Sakai a jihohi domin hakan ya na sanadiyyar rasa rayukan yan sakai masu yawa; inda ya ce a Jihar Katsina an kashe mutum sama da 50. “Ganganci ne ka ce mai Bindigar Toka ya tunkari Mai AK 47 ko AK 49. Tura su kawai ake ye don a kashe su”. Inji Sanata Adamu Aliero.
Sanatan ya kuma bayar da shawarar cewa abin yi shi ne, “Gwamnatin taraiya ta dauki Karin Jam’an tsaro wadatattu kuma a saya mu su kayan aiki na zamani wandanda su ka yi dai dai da barazanar da ake fuskanta domin magance ta”.
Ana sa bangaren, Sanata Babangida Hussaini Dan Majalisar dattawa daga Jihar Jigawa cewa ya yi sun gaji da tattaunawa a kan batum tsaro a Zauren Majalisar Dattawa ba tare da samun wani canji ba, shi ne dalilin da yasa suka ga dacewar su tunkari Shugaban Kasa tun da shi ne shugaban tsaro na kasa domin lalubo bakin zaren ta yadda za a warware matsalar baki daya.
Sanatan ya kara da cewa Majalisar ta yi nazari na abubuwa da suke da alaka da matsalar tsaro wadanda suka hada da talauci da budaddiyar iyakar kasa, da bangaranci da Siyasa da sauran su.
wadanda duk suna cikin abubuwan da aka duba wajen rubuta wadannan rahotanni kafin a gabatar da shi. Saboda haka aiwatar da shawarwarin rahoton zai taimaka kwarai wajen magance matsalar tsaro da ta addabi kasa baki daya.