Daga Imrana Abdullahi
Tsohon shugaban kasar tarayyar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da ya sa ya zabi tsohon shugaban kasa, Marigayi Alhaji Umar Musa ‘Yar’Adua a matsayin magajinsa duk da ya san cewa ba shi da lafiya.
Tsohon shugaban kasar a wata hira da ya yi da jaridar Yanar Gizo mai suna “TheCable” ya musanta zargin da ake masa na cewa da gangan ya sanya ’yan takara masu rauni don son kai.
A cewarsa, ya dauki matakin ne saboda shawarwarin likitoci sun nuna cewa ‘Yar’Adua, wanda aka yi masa dashen koda, ya cancanci zama shugaban kasa.
“Na kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Dakta Olusegun Agagu, mai albarka, domin neman wanda zai gaje ni. Sun yi la’akari da sunaye da yawa kuma sun yi kima mai yawa a kan dukkan mutanen. Sun bayar da shawararsu. Umaru ne kan gaba a jerin sunayen”.
“Babban hujjar da suka bayar ita ce yana da gaskiya kuma ba zai yi sata ba. An tabo batutuwan da suka shafi lafiyarsa kuma na ba da rahoton likitansa ga kwararre don jin ra’ayi. An canza sunan Umaru don kada gwani ya san ko wanene kuma dalilin da yasa nake neman ra’ayinsa.
“Bayan tantance rahotannin, ya ce majinyacin da alama ya yi dashen koda kuma idan haka ne, babu wani abin damuwa kuma zai kasance cikin koshin lafiya kamar kowane mutum. Shi ke nan.
“Dukkan zage-zage da na san zai mutu kuma shi ya sa na goyi bayansa ya zama shugaban kasa karya ne. Wannan shi ne ainihin labarin da na ba ku,” in ji Obasanjo