Home / News / Dan Majalisa Ya Bukaci Gwamnati Ta Samar Da Rijiyoyin Burtsatse A Fika Da Ngelzarma A Jihar Yobe

Dan Majalisa Ya Bukaci Gwamnati Ta Samar Da Rijiyoyin Burtsatse A Fika Da Ngelzarma A Jihar Yobe

 

 

Bashir Dollars, Daga majalisar dokoki ta kasa, Abuja

 

Dan majalisar wakilai ta tarayya Injiniya Muhammad Buba Jajere, ya shawarci Gwamnatin tarayya da ta himmatu wajen samar da ingantattun Rijiyoyin burtsatse da nufin bunkasa harkokin samar da lafiyayyen ruwan sha da na amfanin yau da kullum a garuruwan Fika da Ngelzarma da ke Jihar Yobe domin a kawo karshen matsalar ruwan da suke fama da shi.

 

 

 

Ya dai gabatar da wannan kiran ne bayan gabatar da kudirin da Injiniya Muhammad Biba Jajere  ya gabatar a gaban majalisa a ranar Alhamis.

 

 

 

 

Majalisar ta kuma bayar da shawara ga hukumar raya yankin Arewa maso Gabas (NEDC) da ta shiga cikin aikin samawa wadannan garuruwa da ingantaccen ruwan sha sannan kuma su hada hannu da ma’aikatar ruwa ta tarayya da tsaftace muhalli domin samar da mafita game da wannan batun karancin ruwan sha da ake fama da shi a garuruwan Fika da Ngelzarma a cikin Jihar Yobe.

 

 

 

Honarabul Jajere, ya kuma yi bayanin cewa, garuruwan Fika da Ngelzarma da ke a cikin kananan hukumomin Fika da Fune dukkansu na kunshe da mutane da yawa kuma jama’ar na kara karuwa tsawon shekaru.

 

 

 

 

Kamar dai irin yadda aka san yanayin, ” wurare kamar Fika da Ngelzarma wurare ne da ke da tuddai da kuma kwazazzabai kuma suna da dadadden tarihin matsalar karancin ruwa wanda hakan ya zamar wa mazauna yankin babban kalubale musamman mutanen da ke zaune a garuruwan biyu kuma hakan na yin barazana wajen samun ci gaba a wuraren, musamman a wajen harkokin Noma da kiwon Dabbobi da ya zama manyan hanyoyin rayuwar jama’ar yankin baki daya.

 

 

 

 

Ya bayyana cewa, samun ingantaccen lafiyayyen ruwan mai tsafta ne abin da ake bukata domin samun lafiya da kuma rayuwa mai inganci a tsakanin al’umma, kuma hakan zai taimaka wajen samun kayan amfanin Gona mai yawa domin bunkasar tattalin arzikin kasa da na jama’a baki daya.

 

 

 

 

 

Jajere ya bayyana damuwarsa game da lamarin a don haka ne ya yi kira da cewa ya dace a dauki matakai tare da hadin Gwiwar kananan hukumomi, jiha da Gwamnatin tarayya wajen magance matsalar karancin  ruwa a wadannan garuruwan duk da nufin samawa al’umma sauki.

 

 

 

 

Sai ya ci gaba da bayanin cewa an dauki matakan samun yin aikin hadin kai tsakanin Gwamnatocin kananan hukumomi, Jiha da Gwamnatin tarayya domin ana bukatar samun hakan da nufin magance matsalar Barkewar cututtuka a tsakanin jama’a.

 

 

 

Majalisar ta shawarci kwamitin kula da albarkatun  ruwa na majalisar da kuma hukumar kula da ci gaban yankin Arewa maso Gabas (NEDC) da su tabbatar da bayar da cikakken hadin kai.

 

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.