Home / Uncategorized / Dan majalisar Funtuwa Da Dandume Ya Raba Wa Jama’a Kudi, Kayan Abinci Da Kekunan Masu Bukata Ta Musamman

Dan majalisar Funtuwa Da Dandume Ya Raba Wa Jama’a Kudi, Kayan Abinci Da Kekunan Masu Bukata Ta Musamman

 

 

A kokarin ganin ya ci gaba da tallafawa al’umma domin su samu saukin rayuwa da suke ciki Dan Majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Kananan hukumomin Funtiwa da Dandume Honarabul Barista Abubakar Muhammad Gardi,Ya Raba Kekunan Masu bukata ta musamman guda  100 da Tallafin kudi Naira miliyan (₦8,630,000) ga shugabannin Al’umma da jam’iyya, tare da kayan abinci ga wadanda hare-haren ‘yan ta’adda suka shafa.na al’ummar Funtua da Dandume.

 

A ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025, Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Funtua da Dandume, Honarabul  Abubakar Muhammad Gardi, ya kaddamar da rabon kekunan guragu 100 da tallafin kudi na Naira miliyan (₦8,630,000), ga shugabannin jam’iyya da na al’umma, tare da kayayyakin agaji ga wadanda hare-haren ‘yan ta’adda suka shafa. A kananan hukumomin Funtua Da Dandume.

An gudanar da taron ne a harabar sakatariyar karamar hukumar Dandume, tare da halartar jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (SEMA), wadda ta hada gwiwa da dan majalisar wajen isar da tallafi ga mutane 250 da ke fama da mawuyacin hali. a kananan hukumomin Funtua Dandume.

Kayayyakin da aka rabawa sun hada da shinkafa, masara, manja, magi da gishiri, da sauran kayan bukatu na yau da kullum.

yayin da yake jawabi Hon. Abubakar Mohammad Gardi ya ce, “Wannan kekunan guragu da muka rabawa masu bukata ta musamman na daga cikin kokarinmu na saukaka musu wahalhalu, musamman wajen zuwa makaranta da gudanar da rayuwa cikin sauki.” Ya kuma sha alwashin ci gaba da Hidim tawa al’umma cikin gaskiya da rikon amana.

Shugaban karamar hukumar Dandume, Hon. Bashir Sabiu Gyazama, ya yaba da wannan kokari, Na Hon. Barr Abubakar Muhammad Gardi, yana mai bayyana cewa hakan ya nuna yadda dan majalisar ke damuwa da ci gaban yankinsa. Ya kuma bukaci jama’a da su yi amfani da lokacin Babbar Sallah Idi wajen yin addu’ar samun zaman lafiya ga karamar hukumar da kasa baki daya.

Mutane da dama ne suka tufa albarkacin bakinsu daga ciki har da Hon. Sulaiman Abubakar, kansila mai wakiltar gundumar Jiruwa, da sauransu.”

Taron ya samu halartar wakilan al’umma da dama, wanda suka haɗa da shugabannin jam’iyya APC na kananan hukumomin Funtua Dandume, wadanda suka bayyana goyon bayansu ga dan majalisar tare da fatan alheri a gare shi.

About andiya

Check Also

10,000 South East Pupils Get School Bags From Collins Onyeaji Foundation

    No fewer than 10,000 pupils in the South East Zone of Nigeria are …

Leave a Reply

Your email address will not be published.