Home / Kasashen Waje / DAUDA LAWAL DA SAURAN GWAMNONI SUN HALARCI LIYAFAR CIN ABINCIN DARE DA SHUGABAN KASAR RWANDA, KAGAME.

DAUDA LAWAL DA SAURAN GWAMNONI SUN HALARCI LIYAFAR CIN ABINCIN DARE DA SHUGABAN KASAR RWANDA, KAGAME.

Daga Imrana Abdullahi

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya shirya wa gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal tare da wasu gwamnonin Najeriya liyafar cin abincin dare.

An gudanar da liyafar cin abincin daren ne a birnin Kigali, ranar Asabar, wani bangare ne na taron fadakarwa a kan shugabanci na kwanaki uku da hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) tare da hadin gwiwar kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) suka shirya tare da daukar nauyinsu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta nuna cewa shugaban kasa Paul Kagame ya halarci taron rufewa da aka yi da gwamnonin, mai taken “Jagora wajen tsara makomar “Pan-Africanism and Integration in the Changing World”.

Sanarwar ta  kara da cewa zaman ya dauki sama da sa’o’i hudu inda shugaban kasar Ruwanda ya yi nazari sosai tare da yin musayar ra’ayi da gwamnonin Najeriya, daga bisani suka wuce wajen liyafar cin   abincin dare.

“Taron na kwanaki uku na Shugabancin Zartarwa a Kigali, Ruwanda ya fara ne daga ranar 24 zuwa 26 ga Agusta 2023, UNDP tare da hadin gwiwar kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ne suka shirya kuma suka dauki nauyin.”

“A yayin, gwamnonin sun tsunduma cikin tarukan da suka yi nazari kan nasarar da Rwanda ta samu wajen sauye-sauyen zuba jari a fannin fasahar zamani ta dijital, tsare-tsare na birane, da sauye-sauyen tattalin arziki, tare da tattaunawa ta sirri da shugaba Kagame.

“Don karrama Gwamnonin da suka fito daga Najeriya da suka kawo ziyara, Mai Girma Shugaban Kasar Ruwanda, Paul Kagame ya shirya musu liyafar cin abincin dare.

“Taron ya kasance wata hanya ta karfafa dangantaka da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Rwanda da gwamnatin Najeriya a matakin kasa da kasa.”

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.