Home / Labarai / BAMU AMINCE NAJERIYA TA YAKI NIJAR BA – BUGAJE

BAMU AMINCE NAJERIYA TA YAKI NIJAR BA – BUGAJE

Daga Imrana Andullahi

Dokta Usman Bugaje ya bayyana cewa abin da ake son yi ga kasar Nijar da sunan ECOWAS ba komai ba ne illa kasashen Faransa da Amurka kawai.

Dokta Bugaje ya ce kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta ECOWAS ta rasa shugabanni nagari ne kawai har hakan ta Sanya za a yi amfani da ita domin azo a cutar da jama’a kuma da ake cewa wai kasar Nijar ba Nijar ba ce, an dai son a yaki arewacin Najeriya ne kawai

Dokta Usman Bugaje ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron fadakar da jama’a a kan al’amarin juyin mulkin sojan kasar Nijar da aka yi a masallacin ITN da ke Zariya a Jihar Kaduna Najeriya.

“Saboda haka duk mutumin arewacin Najeriya ya san cewa wannan Yakin idan an yi shi ba Nijar ake yaka ba shi ne wato arewacin Najeriya ake yaka, saboda da an fara Amurka da Faransa su za su yi Yakin domin za su kawo makamansu na yaki domin ba za su iya bambance waye dan Najeriya ko dan Nijar ba, sabida haka yakamata yan kasar mu ta Najeriya su fatka su fito su nunawa wannan shugaban kasar da bai san kasar shi ba su gaya masa cewa wannan Yakin ba zai yuwu ba. In dai da sunan Najeriya yake mulki mune yan Najeriya muke zabe ko mun zabe shi ko ba mu zabe shi ba mune yan kasa muna da hakkin cewa ba mu amince kasar mu ta shiga yaki ba”.

Bugaje ya ce “Yan majalisun mu da muka aika idan suka sake suka bashi izini ya fara yaki ba shakka da su zamu fara Yakin da zarar sun yi sakacin bashi damar yin Yakin, domin ba zamu bari a lalata mu ba kasancewar an san irin arzikin da muke da shi da Allah ya yi mana, an san irin tasirin da nan gaba kadan zamu yi. Kamar yadda aka Sani cewa nan gaba Najeriya za ta kai adadin ta miliyan dari uku idan kuma aka kara wasu shekaru 20 din za ta iya kaiwa miliyan dari hudu da yan kai zuwa da Talatin a wannan lokacin ne za ta kai ta uku a yawan jama’a a duniya bayan kasashen Indiya da Cina don haka idan Najeriya ta kai wannan adadin mu ne masu yawa kasancewar muke aure da yawa kuma mu haihu da yawa ba wata tantama don haka ne ake son kar mu kai ga can din. Domin idan mun kai ga can da irin arzikin da Allah ya ba mu ba wai Amurka ba Faransa ba sai mun wuce duk wata kasa a duniya har Cina sai ta zama albarka, saboda haka wannan shi ake ma hari kada a bar mu mu gane kada mu kai”.

” Ta yaya shugabannin da ba su san kasar su ba kuma ba sa magana da mu sai kawai su nemi kare wata maslaha sai su lalata mana gaban mu wato gaban shekaru 100 nan gaba duk su lalata mana ba zamu bar su ba a gaya masu, kuma idan sun tashi mu zamu fara yakar shugabannin na mu kafin su kai ga Nijar”.

Batun dangantaka tsakanin Najeriya da Nijar kuwa sai Dokta Bugaje ya ce an wuce hakan domin tuni an zama yan uwa kamar Hassan da Usaini, domin ba yadda za a yi a raba Nijar da Najeriya , shin wai shi layin da aka ja tsakanin Najeriya da Nijar ai ba mu muka Sanya shi ba.

Bugaje ya ce don ta shi ne ma idan da jama’a za su iya sai a je a dauke layin sa turawan mulkin mallaka suka shata wajen raba kasashe a Afirka saboda duk da cewa sun yi wa jama’a mulkin mallaka kuma har yanzu ba su tausayin mutane.

” ina ban Sanya layin da aka shata ba na raba kasashen Afirka kuma kakanni na ba su shata ba don haka ban san wanda ya Sanya wannan layin ba don haka ba wata ma’anar hakan”.

Dokta Bugaje ya kuma ce akwai wata shawarar da yake da ita cewa, ” kawai a yunkura a hana wannan shugaban kasar yin bankaura da hauma hauma domin ba zamu bari ayi amfani da shi ba a lalata mana kasa da zumuncin mu ba. Saboda haka a fito manyan mu suyi magana, samarin mu suyi magana duk wata hanyar da aka ga ta dace abi in ma ta kama ayi Zanga Zanga ayi, ace a fito ayi a kuma ce ni na ce ayi hakan.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.