IMRANA ABDULLAHI
AN bayyana irin yadda wasu ke tafiyar da Dimokuradiyya a Najeriya a matsayin wani al’amari mai ban TSORO kwarai.
Honarabul Aliyu Muhammad Waziri da ake yi wa lakabi da Dan marayan Zaki ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta DITV, Alheri radiyo da ke cikin garin Kaduna.
Aliyu Waziri ya ce akwai yadda wadansu abubuwa ke faruwa a harkar siyasa musamman ma a batun masu zaben dan takara a jam’iyyu da ake cewa deliget, ya dace iyayen jam’iyya da dai dukkan Dattawa baki daya su rika yi wa tukka hanci kafin wani lamari ya faru.
“Ta yaya za a Sanya mutum ya zama deliget bayan bai ma san me ake kira da hakan ba, an dai Sanya mutum ne domin kawai ya rika karbar kudi a hannun yan takara kuma kudin nan makudai iyaye da Dattawan jam’iyya na ga ni mutumin da bai ta ba rike dubu Hamsin tashi ta kansa ba sai a bashi miliyan biyu domin shi deliget ne kawai”.
Da irin wannan halin da manyan mu suke ciki ba mu amince da shi ba domin ba abu ba ne mai kyau”, inji Aliyu M Waziri Dan marayan Zaki.
“Ta yaya ribabben abu ya fitar da mai kyau sai dai a jikin mai kyau a fitar da wanda ya rube, ya dace a Sani fa cewa zaben deliget abu ne mai daraja a duk duniya muna fatan irin yadda siyasa ta fara kama kasa ana bukatar ta dore, ba kamar yadda ake da gurbatattun mutane ba masu hadama yunwa da babakere kawai su me za su samu kawai don haka ba mu bukatar irin wannan shugabancin
Kuma ta yaya za a ba mayunwaci gadin abinci, ai duk a cikin PDP ba wanda ya kai Atiku cancantar ya zama dan takarar shugaban kasa amma sai ga wasu sun yi wani dan rukuni su kadai kawai
Ku ya dace a Sani cewa a kan matsalar deliget na kasa guda daya daga karamar hukuma za a iya rushe zaben baki dayansa, kuma a ina aka samu a rika yin ciniki da masu zaben dan takara har a rika ba su makudan kudi domin su zabi wani dan takara shin lamarin kasuwanci ne.
Ta yaya za a zabi ingantaccen shugaban kasa da zai yi wa kasa aiki bayan mutum ya Sanya kudi ya biya su ka kuma Sani cewa na sayar da gida ko fili ko dai wata kadara ko na bi wata hanya ne na samu kudin
“Haka fa shugaba Yar Aduwa ya rika yin magana a game da harkar cin Amana da sunan siyasa to, da ya na da rai da a yanzu kuka kawai zai fashe da shi saboda irin yadda ake gudanar da harkar a gurbace ba bin tsarin da ya dace.
” A nan gaba duk wanda zai yi takara ya shiga uku na biyu kuma shima deliget din sai ya san abin da zai nema domin an bude wata kafar da bata da kyau a cikin al’ada da addini sam