Home / News / DOLE IYAYE SU KULA DA TARBIYYAR YAYANSU – MAGAJIN QWARA

DOLE IYAYE SU KULA DA TARBIYYAR YAYANSU – MAGAJIN QWARA

Matukar Iyaye Ba Su Sa Ido Akan Tarbiyyar ‘Ya Yan Su Ba, To Akwai Matsala A Makomar Su.. Magajin Qwara..
Sani Gazas Chinade
Daga Damaturu
Babban mai fafutukar yaki da masu aikata laifuka a Azare, Ahmed Muhammed Qwara da aka fi sani da Inkuji ya ce matukar dai iyaye ba su sa ido kan tarbiyyar ‘ya’yansu ba, to ba za su yi tunanin makomar rayuwarsu ba.
A cewar sa a kwanakin nan da yawa daga cikin matasa suna ta’ammali da shan miyagun kwayoyi ma su sa maye da ke haifar da aikata muggan laifuka alhali akasarin iyaye da masu kulawa da su suna kallon su ba tare da daukar mataki akai ba.
Da yake zantawa da wakilinmu a garin Azare, magajin marigayi fitaccen dan gwagwarmaya Ahmed Muhammed Qwara wanda kuma shi ma  zuriyar jinin su daya da Marigayi Ali Kwara, ya bayyana cewa kusan a kullum, tawagarsa na daukar dawainiyar matasa da dama da ake kamawa da muggan kwayoyi da kananan laifuka a wurare da dama a  jihar Bauchi ta wajen kokarin Canza musu halayyar su kasancewar muddin ba’a yi hakan ba kan iya zama barazanar a cikin al’umma wajen aikata laifuka, wanda hakan zai haifar da rashin  zaman lafiya a kasa.
Ahmed Muhammed Qwara ya ce yana aiki da rundunar ‘yan sanda domin kamo masu aikata laifuka iri-iri da ‘yan sanda ke gurfanar da su a gaban kotunan shari’a, inda ya yaba wa Gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammed;  Sufeto Janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya da mai martaba Sarkin Katagum, Alhaji Umar Kabir Umar bisa jajircewarsu wajen ganin an dawo da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Mai Yaki da Laifukan ya bayyana cewa a baya-bayan nan, ya taimaka wa ‘yan sanda wajen danke masu aikata laifuka da dama a lokacin da suke zirga-zirga don dakile masu  ayyukan yin garkuwa da mutane a Bauchi da jihohin da ke makwabtaka da su ta yadda za a samar da zaman lafiya a wuraren da abin ya shafa.
Da wakilinmu  ke tambayar sa kan duk wata matsala da za ta iya hana samun nasarar yaki da miyagun laifuka a Kasar, sai ya amsa  cikin nadama ya ce da yawa daga cikin masu aikata laifuka sun samu kudade ta yadda a duk lokacin da aka kama su aka gurfanar da su a gaban kotu, sai su biya lauyoyinsu kudade masu tsoka don shiryawa.  don belin su, wanda zai ba su damar komawa mataki na aikata laifuka
Ya yarda cewa wannan aiki nasu na yaki da masu aikata laifuka  yana da matukar kalubale a fannin fasaha da kudi amma ya tabbatar da cewa shi da tawagar sa za su ci gaba da kasancewa cikin halin  jajircewa da kuma mai da hankali wajen ganin sun ci gaba da rike gadon da marigayi Ali Muhammed Qwara ya bari, yana mai imani da cewa da irin addu’o’in da jama’a suka saba yi da irin gudunmawar da suke bayarwa tare da kbayanai da suke samu na masu aikata laifuka za su ci gaba da kasancewa masu samun nasara akan ayyukan su in Allah SWT ya so. 

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.