Home / Labarai / DOLE NE MUTANE SU CI KWAKWA – SHEHU SANI

DOLE NE MUTANE SU CI KWAKWA – SHEHU SANI

Ina Masu Zaben Taliya Da Indomi

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna, Arewacin Najeriya

Tsohon Sanatan yankin Kaduna ta tsakiya Kwamared Shehu Sani ya yi kira ga Gwamnati a dukkan mataki na Najeriya da su kula duk irin matakan da za su dauka ya zama akwai Tausayi, Jinkai da kula da jin dadi da walwalar jama’a.

Kwamared Sanata Shehu Sani ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Sallah a gidansa da ke Unguwar Sarki cikin garin Kaduna.

Kwamared Sanata Shehu Sani, ya ci gaba da cewa a halin da ake ciki a yanzu da yawan jama’a na cikin akuba da sauran nau’uka na shiga cikin mawuyacin hali, har ta kai wasu ba su iya biyan kudin makarantar yayansu, wasu ko abincin da za su ci ma babu kuma ba su iya biyan kudin asibitin iyalansu Mata ko na yayansu da yawa daga cikin al’umma ba su iya taimakawa iyayensu.

Sanata Shehu Sani ya kara da cewa wannan ba shi ne al’ummar da muka yi Gado ba tun iyaye da kakanni da suka gabata.

“Mafi yawan mutane a halin yanzu da ke kan madafun iko sun more tare da jin dadin yin ilimi kyauta tun suna yan kananan yara, sun kuma ji dadin zama cikin kwanciyar hankali da lumana.

“Irin matsalolin rashin tsaron da muke fuskanta a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon rashin adalci da samun dai- daito a tsakanin al’umma, idan mutum daya ya na da abin da bashi da misali ko iya amma kuma wani ba shi da komai. Wanda da bashi da komai ba abin da zai rasa ko yin asara, kuma sai idan Talakawa na cikin natsuwa ne sannan masu kudi za su iya kwanciya har suyi bacci, ya dace hakan ya zamo darasi a rayuwar mu.

Kwamared Shehu Sani ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar musulmi manya da yara da su yi rayuwa bisa yin koyi da umarnin Annabin tsira Muhammadu SAW, wanda shi ne fiyayyen halitta .

Saboda duk wanda ya bi wannan hanya hakika ya samu zaman lafiya tare da kwanciyar hankali a rayuwa.

Kuma sako ga musulmi da yan kasa baki daya shi ne ” shi ne na farko kowa ya cire Kwadayi da son zuciya a rayuwa, saboda idan al’umma na da Kwadayi za su zama bayi kuma mabarata, sannan idan al’umma na da Kwadayi za su wulakanta a wurin shugabanni kuma idan da Kwadayi ba su da alkibla a rayuwa.

Abu na biyu shi ne sako na ga mutanen da suke kan mulki, idan mutane suka zabe ka a matsayinka na shugaba dole ayi wa kowa adalci da kwatanta gaskiya a wajen tafiyar da mulki domin mulkin da mutum ya samu Allah ne ya ba mutum ta hanyar yin zaben jama’a.

Saboda akwai mutane Dubbai da ke nema amma ba su samu ba sai Allah ya zabe ka ya baka.

“Duk wani gyara da za a yi a kasa a duba cewa Talaka ne ya wahala ya yi zabe don haka a samar masa sauki”.

” Irin sace – sacen da aka tafka a Gwamnatocin baya da Gwamnatin da ya gabata ya zama wajibi masu mulki a halin yanzu su kwatowa Talakawa yancinsu a kan mutanen da suka yi sata da suka zalunci talaka. Duk abin da wanda aka zaba ya dace ya zamo mai yi wa talaka aiki ne, ba kawai an zabi mutum sai ya aikata gaban kansa ba”.

Kuma ina muka fito a shekaru Takwas da suka gabata ba mu cewa Allah ya zaba mana shugaba sai dai kawai jama’a suce su wane suke so kawai sai da aka fifita wannan mutum ya zama mutumin da baya yin laifi sai ga shi an shekara Takwas mulkin ya gagara abubuwan da aka ce za ayi maganinsu an kasa yi.

Yan Ta’adda sun addabi kasar nan a sace mutane har ta kai ga manoma da suke a karkara ba su iya zuwa Gonakinsu saboda gudun yan ta’adda haka nan yara yan makaranta ba su iya zuwa saboda yan ta’adda. Kuma an ciyo bashin da ba a taba ci ba a tarihin Najeriya, sannan ayyukan da aka ce za a yi an yi kadan an bar mu da dimbin bashi ga kuma Kangayen gine gine nan kala kala kuma ga shi wadanda suke son su hau kan mulki ba su hau ba sai wadanda ba su so ne suka hau.

Shehu Sani ya ce tabbas muna daya daga cikin wadanda muka cucina kan mu wajen yin zabe da ba a nemi zabin Allah ba sai na son zuciya kawai sai muka fifita shugabanni kamar basa yin laifi.

Kiran kuma da zan yi ga Talakawa shi ne ka Sani duk shugaban da ka zaba kamar Macen da ka aura ne da dadi ba dadi haka zaku zauna, saboda haka ne ake cewa idan zaku yi zabe to, ku kaucewa Kwadayi.

“A zaben da ya gabata an nuna kwadayi an karbi Indomi an amshi taliya, to, yanzu lokaci ne da za a ci kwakwa, saboda haka duk abin da ka gani ka Sani idan ka zabi shugabanni tsakani da Allah, Allah zai kawo maka sauki amma duk wadanda suka yi zaben taliya, Shinkafa da Indomi duk abin da ka gani kai ka jawo wa kanka”, inji Sanata Shehu Sani.

Kuma babban kiran da zamu yi a matsayin mu na yan kasa shi ne ya zama wajibi jama’a su cire tsoro a cikin zuciyarsu, idan shugabanni sun kauce a gaya masu gaskiya. “Malaman addini ba a nemanku sai lokacin zabe don haka yakamata ku dinga yin amfani da mumbari wurin wayar da kan jama’a ta wajen kauda jama’a ga Kwadayi, kauda jama’a ga tayar da husuma. A kuma fadakar da jama’a a kan amfanin hadin kai da taimakon Juna a tsakanin al’umma da sanin mutuncin Juna

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.