Home / Big News / Dole Sai An Samu Cikakken Hadin Kai Da Zaman Lafiya A Samu Ci Gaban Da Ake Bukata – Sarkin Zazzau

Dole Sai An Samu Cikakken Hadin Kai Da Zaman Lafiya A Samu Ci Gaban Da Ake Bukata – Sarkin Zazzau

Daga Imrana Abdullahi
…..Najeriya Na Fuskantar Matsalolin tattalin arzikin da na tsaro, inji Munnir Jafaru Madakin Zazzau
Honarabul Ibrahim A Musa Bamalli Madakin Gonar Zazzau, represents the emir of Zazzau Alh Ahmad Nuhu Bamalli, Kira ya yi da cewa hat fa sai mun yi abin da ya dace domin mu samu nasarar samun abin da muke bukatar a kasa tarayyar Najeriya da idan Allah ya so za ta wuce kowace nahiyar a cikin nahiyoyin duniya Baki daya.
Ya bayyana hakan ne a wajen Taron shekara shekara na Kasuwar duniyar ta Kaduna Karo na 51 da ya gudanar a Babban dakin taro na Kasuwar da ke Kan hanyar Zariya a Unguwar Rigachikun Kaduna.
Sarkin Zazzau ya ci gaba da bayanin cewa hakika tare da hadin Kai da taimaki da ganin girman juna tare da Jin tsoron Allah a hada Kai, musamman hadin Kan kasa da Yan kasa Baki daya.
Kada mu Bari wadanda BA su da kishin kasa KO kishin Yan kasa su lalata kasar nan, mu hada Kai mu Zama Abu daya, koda Kasuwar nan said an hada Kai da zaman lafiya sannan a samu vi gaban da Ake bukatar, dole a Fadi gaskiya KO Mai dacinta
Hakika Mai kartaba Sarkin Zazzau ya umarce ni da in ISAR da sakon gaisuwa da kuma fatan a samu dubun alkairin da ke cikin wannan shugabanci da aka samu a halin yanzu
Alhaji Munnir Jafaru Madakin Zazzau, ya bayyana Najeriya a matsayin kasar da ke fama da matsalolin tsaro da tattalin arzikin kasa.
Inda ya ce hakika masu kaiwa Jama’a Hari na kokari a koda yaushe su kaiwa Jama’a Hari har su kashe BA tare da yin la’akari da KO mutum Musulmi ne KO Kirista ba ne musamman masu akidar Boko haram duk suna nan.
Alhaji Munnir Jafaru ya bayyana hakan ne a lokacin da Yake Gabatar da jawabin a wajen Taron shekara shekara na Kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna, inda aka samu sabon shugaban da zai Jagiranci harkokin kasuwar Baki daya.
Ya kuma yi godiya da shugaban Kasuwar mai baron gado Sakamakon irin namijin kokarin da ya yi wajen tafiyar da harkokin kasuwar duk da matsalolin da ya fuskanta.
Alhaji Munnir Jafaru Madakin Zazzau Kira ya yi a madadin Kasuwar duniyar kasa da kasa ta Kaduna da cewa kananan hukumomi da su yi amfani da makudan kudin da suke samu daga Gwannatin tarayyar Najeriya
Ya kuma yi Kira ga Gwannatin tarayya da ta yi duba da idanun basira a game da damar da ta BA wadansu su shigo da kayan amfanin Gona duk da irin kokarin da manoman Najeriya ke yi na Samar da abinci a kasa don haka muna yin Kira da a duba wannan don Kada a karya gwiwar Manoma a nan gaba.
“Muna yin godiya ga Gwannatin jihar Kaduna da ta mayarwa da wannan hukumar Kasuwar duniyar ta kasa da kasa da takardun mallakar wannan wuri mina godiya kwarai saboda mun San irin yadda muka Shiga a wajen a dawowa da wannan kasuwar da takardun ta.
Jerry Adams, shugaban hukumar Tara kudin haraji na Jihar Kaduna,
A wannan hukumar ta Tara kudin haraji muna matukar farin jiki da takama da wannan kasuwar duniya ta kaduna
Mu a jihar Kaduna mun San cewa biyan haraji me kaidai abin da za mu samu kudin Shiga ganin cewa maganar fetur ta Zama tarihi.
“Muna yin aiki tukuru kwarai domin mu yi amfani da abubuwan da muke da Shi a cikin jihar Kaduna domin samun nasarar tara haraji,Wanda saboda hakan ne ya sa aka samu canza Dokokin haraji guda hudu.
Muna yin Kira ga masu yin harkokin kasuwanci da su bayar da hadin Kai da goyon baya GA wadannan Dokokin haraji guda hudu da aka Samar.
Muna Tara wannan kasuwar kasa da kasa murnar samun yin wannan taron na Karo 51
A jawabinsa na godiya Faruk Suleiman,.ina godiya kwarai GA duk Wanda ya zo wannan taron musamman ma ga shugabannin mu da suka yi aiki tukuru har wannan kasuwar duniya ta kasa da kasa ta zamo a cikin Hali da yanayin da take a halin yanzu.
Ina godiya GA wadanda muka yi aiki tare da su a tsawon lokacin da ya gabata.
.

About andiya

Check Also

Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861 Ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.