Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da korar Bello Zubairu Idris, magatakardar majalisar dokokin jihar Kaduna. An bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar
Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da korar Bello Zubairu Idris, magatakardar majalisar dokokin jihar Kaduna.
Muyiwa Adekeye mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa ya bayyana hakan.
Adekeye ya ce gwamnan ya kuma amince da sallamar Yau Yunusa Tanko, babban sakatare, da Francis Kozah, sakataren hukumar bunkasa kasuwanci ta Kaduna (KADEDA) daga aiki.
Ya kara da cewa gwamnan ya kuma amince da murabus din Stephen Joseph, babban sakatare a Jihar
A makon da ya gabata ne El-Rufai ya sha alwashin ci gaba da rusa gidaje da kuma “cire miyagun mutane” har zuwa awa 11, da zai yi a kan karagar mulkin jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da wani littafi kan abubuwan da ya gada.
Mista Emmanuel Ado, wani gogaggen dan jarida kuma mai sharhi kan al’umma ne ya rubuta littafin mai suna, “Sanya Jama’a Farko”.
Ya ce, “Duk wani abu mara kyau da muka samu, za mu cire shi, don kada gwamna mai zuwa ya sake yin hakan.
A kula har zuwa awa na sha ɗaya lokacin da za mu bar ofis. Za mu ci gaba da korar miyagu tare da kawar da munanan abubuwa.”
Gwamnan ya bayyana haka ne kwana guda bayan da gwamnatinsa ta kwace ikon mallakar wasu kadarori 9 mallakar tsohon gwamnan jihar Ahmed Makarfi, tare da sanya su ajerin wadanda za a ruguje.