Home / Labarai / Farfesa Gwarzo ya taya Jarumin Kannywood, Ali Nuhu murnar zama shugaban Hukumar shirya fina-finai ta Nijeriya 

Farfesa Gwarzo ya taya Jarumin Kannywood, Ali Nuhu murnar zama shugaban Hukumar shirya fina-finai ta Nijeriya 

Daga Imrana Abdullahi
Shugaban gamayyar rukunin jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya fitaccen jarumin fina-finan Nijeriya kuma furodusa Ali Nuhu murnar nadin da aka yi masa a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Fina-Finan Nijeriya.
Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Gwarzo ya sanyawa hannu da kansa kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Juma’a.
Farfesa Gwarzo ya bayyana nadin fitaccen jarumin a matsayin nadin da ya dace ganin irin gudunmawar da ya bayar a harkar fim a kasar nan.
Ya bayyana kyakkyawan fatansa na cewa duba da irin dimbin gogewarsa da hazakarsa da basirarsa, fitaccen jarumin fina-finan na Nollywood zai daukaka Hukumar zuwa babban matsayi.
“Shugaba Tinubu ya nada wanda ya dace ya shugabanci Hukumar, la’akari da cewa Ali Nuhu Darakta ne, kuma mai tsara labari ne, kuma mai koyar da rawa ne, wanda ya yi tasiri sosai a masana’antar fim ta Kannywood.
“A madadin kaina da gamayyar rukunin Jami’o’in Maryam Abacha American University, ina so in bi sahun sauran ‘yan Nijeriya wajen taya ka murnar wannan nadi,” in ji Farfesa Gwarzo a cikin sanarwar.
Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya bai wa sabon shugaban Hukumar ta Fina-Finai ta Nijeriya damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansa bisa gaskiya tare da nufin kai Hukumar zuwa babban mataki.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.