Daga Imrana Abdullahi
Sakamakon yin la’akari da kokarin taimakawa rayuwar al’umma da kuma jibintar harkokinsu yasa Gidauniyar taimakawa marayu, gajiyayyu,masu bukata ta musamman da kuma daukar nauyin yara dalibai yan makaranta, Gudauniyar A A Charity ta Karrama kwamishinan ma’aikatar kula da kananan hukumomi na Jihar Kebbi Honarabul Abubakar Garba Dutsinmari, Sardaunan Bagudo kuma Majaen Gwandu da lambar karramawa ta gudanar da ayyukan jin kai.
An dai bayar da wannan lambar karramawa ne a wajen wani babban taron da Gidauniyar ta shirya kuma ya gudana a garin Kaduna Arewa maso Yammacin Najeriya.
A wajen babban taron Gidauniyar A A Charity, an kaddamar da shugabannin da za su ja ragamar tafiyar da al’amuran gidauniyar wadda Umar Sama’ila Dankal, ke zaman babban Sakataren Gidauniyar na kasa.
Kuma Gidauniyar za ta bude sauran dukkan ofisoshin su da ke daukacin Jihohi da dama nan bada jimawa ba.
Ya’u Nepa Kamba ne ya wakilci Kwamishinan ma’aikatar kula da kananan hukumomi na Jihar Kebbi Honarabul Abubakar Garba Dutsinmari da ya karbi lambar karramawar a madadin kwamishinan.