DAGA IMRANA ABDULLAHI, a arewacin Najeriya
Sabanin irin cece – kucen jita – jitar da ake ta yadawa a tsakanin al’ummar Jihar Zamfara cewa wai Gwamnan Jihar Dokta Dauda Lawal ba su gaisa da shugaba Bola Ahmad Tinubu ba a lokacin da ya kai wata ziyara domin nemowa jama’ar Jihar mafita game da harkar matsalar taarin da ke addabar Jihar.
Kamar dai yadda kowa zai iya gani kuru kuru da idanunsa a cikin wannan hoton bai bayar da cikakken bayanin da kowa zai Gamsu cewa wannan magana ba haka take ba domin Gwamna Dauda Lawal ya gana da shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmad Tinubu kuma kamar yadda hoton ya nuna dukkansu suna cikin murna da farin cikin gaisawa da Juna.
Sai kuma wani hoton shima da ke nuna irin yadda Gwamna Dauda Lawal ke cikin jerin Gwamnonin arewacin kasar gida Bakwai (7) da suka ta fi fadar shugaban Najeriya domin tattaunawa da shi a kan hanyoyin da za a magance matsalar tsaron yan bindiga da masu satar jama’a da ke yi wa harkar Noma da yankin baki daya barazana..
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal tare da wasu Gwamnonin yankin arewa maso yamma a ranar Alhamis sun ganawar sirri da shugaba Tinubu.
Ganawar da aka yi a fadar shugaban kasa ta kasance tattaunawa tsakanin shugaban kasa da gwamnoni bakwai (7) na Arewa maso Yamma.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar da aka rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce gwamnonin sun gana da shugaban domin tattauna matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
Gwamnonin sun je fadar shugaban Najeriya ne domin taron Majalisar tattalin Arzikin Kasar wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya jagoranta.
“Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, tare da wasu gwamnonin Arewa maso yamma sun yi ganawar sirri da shugaba Tinubu.
“Taron na daya daga cikin kokarin da Gwamnonin ke yi na neman Shugaban kasa ya sa baki wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma.
“Gwamnonin sun yi wa shugaban kasa bayanin manyan damuwarsu kan matsalolin tsaro da ba za a iya magance su ba a jihohinsu.
“Kafin ganawa da shugaban kasa, gwamnoni bakwai (7) na Arewa maso yamma sun halarci wani babban taron da ya samu halartar gwamnonin jihohi 36.”