Home / Big News / Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Na 58 A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Na 58 A Zamfara

 

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama wani muhimmin tarihi a tafiyar shugabancinsa.

A ranar Litinin ne gwamnan ya jagoranci wannan zama na 58 a zauren majalisar da ke Fadar Gwamnati a Gusau, inda aka tattauna manyan batutuwan ci gaban jihar tare da yanke muhimman shawarwari da amincewa da ayyukan da suka shafi jin daɗin al’ummar Zamfara.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa a shekarar 2025 kaɗai, Gwamna Lawal ya jagoranci zaman majalisar zartarwa guda 23, lamarin da ke nuna irin ƙarfin kulawa da jagoranci da yake bai wa harkokin mulki.

A cewar sanarwar, tun bayan rantsar da shi a watan Mayun 2023, Gwamna Lawal ya kasance kan gaba wajen jagorantar majalisar, inda ya jagoranci zaman 13 a shekarar 2023, sannan 22 a shekarar 2024, kafin a kai ga 23 a shekarar nan ta 2025. Wannan ya kai adadin zaman da ya jagoranta zuwa 58 baki ɗaya.

Sanarwar ta ce, a waɗannan zaman majalisar, ana tattauna muhimman manufofi da tsare-tsaren gwamnati, ciki har da Shirin Ci Gaban Jihar na Shekaru Goma, tare da amincewa da ayyukan raya ƙasa da dama da ke shafar fannoni irin su ilimi, lafiya, ababen more rayuwa, tattalin arziki da tsaro.

Gwamnatin ta ƙara da cewa, yawancin ayyukan da majalisar ta amince da su sun kammala ko kuma suna kan hanyar kammalawa.

Daga cikin manyan ayyukan da aka ambata akwai Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa, wanda ke daf da kammaluwa, da kuma gyare-gyare da sabunta kayan aiki a asibitocin gwamnati a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Haka kuma, an ambaci gini, gyarawa da samar da kayan aiki ga makarantu sama da 500 a faɗin jihar, tare da gina hanyoyin cikin gari a Gusau da sauran ƙananan hukumomi.

Gwamnatin ta ce, waɗannan ayyuka sun haifar da gagarumin canji da ci gaba da jama’a ke gani a sassa daban-daban na jihar.

Da wannan zama na 58, gwamnatin ta bayyana cewa Gwamna Dauda Lawal ya bambanta kansa a cikin takwarorin sa, inda ya zama gwamnan da ya fi kowa jagorantar zaman majalisar zartarwa a cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata.

About andiya

Check Also

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

  Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.