Home / Uncategorized / Gwamna Dauda Lawal Ya Kammala Biyan Hakkin Ma’aikatan Jihar Da Suka Bar Aiki

Gwamna Dauda Lawal Ya Kammala Biyan Hakkin Ma’aikatan Jihar Da Suka Bar Aiki

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya kammala biyan bashin haƙƙin ma’aikatan da suka bar aiki na shekara da shekaru, tun daga shekarar 211, wanda ya kama Naira 9,357,743,281.35.
In dai za a iya tunawa, tun a watan Faburairun nan da ya gabata ne Gwamnan ya amince da a fara biyan basukan na Garatutin tsoffin ma’aikatan.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa gwamnatin Zamfarar ta riga ta kammala biyan bashin Naira 4,860,613,699.22 rukuni-rukuni 9.
Haka kuma sanarwarta ce an biya tsaffin ma’aikatan Ƙananan Hukumomin jihar bashin su na Naira 4,497,129,582.13
Idris ya ce: A jajircewarsa na ganin ya inganta aikin gwamnatin jihar Zamfara, a watan Faburairu Gwamna Lawal ya ƙaddamar da wani kwamitin da zai tantance duk ilahirin tsaffin ma’aikatan jihar da ba a biya su haƙƙoƙin su ba, tun daga shekarar 2011.
“Ya zuwa yanzu, cikin mutum 3,880 da aka tantance, mutum 2,666 sun karɓi haƙƙoƙin su, wanda ya kai ma Naira 4,860,613,699.22, daga cikin basukan da aka biyo gwamnatocin baya. An biya waɗanda suka bar aiki daga shekarar 2015 zuwa 2024.
“A ɗaya ɓangaren kuma, mutum 3,840 cikin ma’aikatan Ƙananan Hukumomi da Malaman Firamare 4,804 da aka tantance sun karɓi haƙƙoƙin su a rukunai 9, wanda ya kai ma kuɗi Naira 4,497,129,582.13. Haƙƙoƙin barin aiki na Garatuti da Ƙananan Hukumomi ke bi ya kai ma Naira 5,688,230,607.20, wanda yanzu haka an biya Naira 4,497,129,582.13. Waɗanda suka bar aiki a tsakanin shekarun 2011- 2021 ne suka amfana.
“A taƙaice dai, ya zuwa yanzu gwamnatin jihar ta biya Tsoffin ma’aikatan jiha da na Ƙananan Hukumomi da ya kai ma Naira 9,357,743,281.35 daga baussukan Naira 13,784,179,513.80 da tsaffin ma’aikatan suka biyo, wato Mutum 6,506, cikin mutum 8,684 da aka tantance. Su ne kuma waɗanda suka bar aiki a tsaknin shekarun 2011- 2024.”

About andiya

Check Also

PCRC Kaduna: Now that the eagle has landed

      By Bashir Rabe Mani     The need for security has indeed …

Leave a Reply

Your email address will not be published.