A ranar Talatar da ta gabata ne Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da Majalisar Gudanarwa da shugabannin jami’o’i guda shida mallakin Jihar Zamfara.
Majalisar da shugabannin da aka ƙaddamar sun haɗa da Jami’ar Jihar Zamfara, Talata Mafara, Kwalejin Abdu Gusau Polytechnic, Talata Mafara, da Kwalejin Ilimi ta Maru.
Sauran cibiyoyin sun haɗa da Kwalejin Jinya da Ungozoma, Gusau; Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya, Tsafe; da Kwalejin Noma da Kimiyyar Dabbobi, Bakura.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce Kundin Tsarin Mulki na majalisar da shugabanninta yana rubuce a cikin wata farar takarda, don sanin irin yadda ya kamata su gudanar da ayyukansu cikin tsari.
Sanarwar ta ƙara da cewa, takardar ya yi nazari sosai kan cibiyoyin ilimi mallakin gwamnatin jihar.
A nasa jawabin, gwamna Lawal ya jaddada cewa taron na nuni da wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarin gwamnatinsa na ceto bangaren ilimi na jihar daga durƙushewa.
Ya ce: “Majalisar da shugabannin da aka ƙaddamar a yau ana sa ran za su inganta harkokin gudanarwar jami’o’inmu sosai. Ta hanyar yin amfani da ƙwarewa, kuma ba shakka sadaukarwar waɗannan fitattun mutane muna tsammanin zai kawo sabon zamani na ilimi a jami’o’inmu.
“A cikin watanni 20 da suka gabata, mun ɗauki ƙwararan matakai don magance barakar da ke faruwa a fannin da kuma dawo da martabar ilimi da aka rasa a jihar.
“Wasu daga cikin waɗannan matakan sun haɗa da gagarumin sake ginawa, gyarawa, da kuma samar da kayayyakin a makarantun firamare, Sakandare, da manyan makarantun gaba da sakandare a jihar, da kuma biyan basukan kuɗaɗen jarrabawar WAEC da NECO.
“Gwamnatina ta kuma ware wasu kuɗaɗe domin sauƙaƙa damar samun tallafin da ake buƙata daga abokan hulɗar ci gaba; Daidaita lamunin albashi, fansho, da alawus-alawus ga ma’aikatan gwamnati da waɗanda suka yi ritaya, ciki har da malamai, da kuma gaggauta biyansu albashi da fansho na wata-wata.
“Domin ci gaba a kan waɗannan da kuma ɗimbin nasarorin da aka samu, mun naɗa nagartattun mutane masu ɗimbin ilimi da gogewa a fannin ilimi da kuma tabbatacciyar tarihin da za su yi aiki a matsayin shugabanni da mambobin Majalisar Gudanarwa na jami’o’i guda shida mallakin jihar.
“Idan aka yi la’akari da yadda Majalisar Gudanarwar ta kasance, a bayyane yake cewa kowane ɗaya daga cikin waɗannan fitattun mutane ya fahimci abin da ake buƙata don gudanar da gagarumin aikin da ke gabansa.
“Gwamnati da al’ummar jihar Zamfara na kyautata muku zato, kuma ko shakka babu kun dace da wannan muhimmin aiki. Matsayinku na da muhimmanci wajen magance ƙalubale daban-daban da ke fuskantar jami’o’i a jihar.
Gwamnan ya taya mambobin majalisar da shugabanni murna, sannan ya buƙace su da su yi amfani da ɗimbin gogewar da suke da shi wajen ciyar da cibiyoyinsu gaba.
“Wannan ya kamata ya haɗa da ƙoƙarin haɗin gwiwa da haɗin kai tare da abokan hulɗa don magance ƙalubalen kuɗaɗe.
“Da waɗannan kalamai, nake alfaharin ƙaddamar da Majalisar Gudanarwa da shugabanni na waɗannan manyan makarantun jihar guda shida mallakar gwamnati a jihar Zamfara a hukumance.”