Related Articles
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayar da tallafin karatu ga haziƙan ɗalibai 30 na Zamfara a makarantar Gwamnatin Tarayya da ke Suleja.
Gwamna Lawal ya yi wannan alwashin ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da ya karɓi baƙuncin haziƙan ɗaliban Jihar Zamfara da kuma Shugabannin Cibiyar Ci Gaban Mata da Matasa ta Muhammad Kabir Danbaba a gidan gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce cibiyar Muhammad Kabir Danbaba ta taka rawar gani wajen ganin Jihar Zamfara ta zama jihar da ta yi fintinkau a Arewan Nijeriya a jarrabawar Hukumar Shirya Jarrabawa ta Ƙasa (NECO) ga ɗalibai masu hazaƙa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, da yawa daga cikin ɗaliban da suka fi samun maki a jarrabawar sun fito ne daga makarantun gwamnati.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya taya ɗaliban da iyayensu murnar sanya Jihar Zamfara alfahari. “Babban aikin da ku ka yi alama ce mai kyau cewa ayyana dokar ta-ɓaci da gwamnatinmu ta yi a ɓangaren ilimi bai faɗi ƙasa banza ba.
“A baya, Zamfara ta kasance a ƙarshen baya a kan harkar ilimi a Nijeriya. Wannan ne ya sa na ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi a bara.
“Muna gyaran makarantu sama da 300 tare da samar masu da cikakken kayan aiki a dukkanin ƙananan hukumomi 14 na jihar. Bugu da ƙari, mun aiwatar da matakan horar da malamai don inganta ilimin makarantun gwamnati.
“Ina so in nuna ƙwarewar da na samu na halartar makarantun gwamnati. Ni kaɗai ne a gidanmu na yi makarantar gwamnati domin na tashi ne a hannun kakanni na a Katsina. Bayan na yi firamare na yi makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kachia, yayin da duk ’yan uwana na zuwa Kwalejin Kings ko Kwalejin Gwamnatin Tarayya. Don haka, muna kan manufar farfaɗo da ingancin makarantun gwamnati.
“Ina so in sanar da cewa ina bayar da cikakken tallafin karatu ga duk ɗalibai 30 masu hazaƙa. Babu iyaye da za su biya komai; tallafin karatun zai ɗauki nauyi duk kuɗaɗe. Wannan mafari ne, yayin da mu ke shirin ci gaba da bayar da wannan tallafin ga ɗaukacin ɗalibanmu.”
Tun da farko, Alhaji Sarkin Pawa Malami, shugaban Cibiyar Ci Hababan Mata da Matasa ta Muhammad Kabir Danbaba, da Arch. A. A Gusau wanda shi ne mai kula da cibiyar ya yi bayani dalla-dalla a kan ayyukan cibiyar tare da ba da shawarar hanyoyin da gwamnatin jihar za ta bi wajen bunƙasa ayyukanta.