Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon kuɗaɗe don tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a jihar.
Rabon kuɗaɗen wani ɓangare ne na Farfaɗo da Ayyukan Tattalin Arziki da suka durƙushe a sanadiyyar COVID-19 na ‘NG-CARES’, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Garba Nadama, Sakatariyar JB Yakubu a Gusau.
Shirin kyautata jin daɗin jama’ar ya shafi masu ƙaramin ƙarfi 44,000 a faɗin ƙananan hukumomi 14 a wani ɓangare na shirin Gwamnatin Jihar Zamfara.
A yayin ƙaddamar da shirin miƙa tallafin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa za a raba Naira Miliyan 4,964,000,000 ga masu ƙaramin ƙarfi a matsayin waɗanda za su amfana.
Gwamnan ya jaddada cewa, ta hanyar ƙaddanar da shirin kyaitata jin daɗin jama’a, jihar Zamfara ta samu ci gaba mai ma’ana, inda sama da mutane miliyan 1.1 suka ci gajiyar shirin a sassa daban-daban.
“Waɗannan nasarorin sun samu ne daga Hukumar Cigaban Al’umma tamu, Fadama III Project, da ma’aikatar kasuwanci da dai sauransu.
“Shirin ya ba da sakamakonbda ake so, kuma an yi shi cikin tsari, tare da samun kusan Naira biliyan 64 a cikin zagaye uku. Wannan nasara ce ta sa jiharmu ta samu karbuwa a matakin ƙasa.
“Na ratsa ɗaukacin ƙananan hukumomi 14 na jihar domin ƙaddamar da shirin Farfaɗo da Tattalin Arziki na COVID-19 a ƙarƙashin ƙungiyar FADAMA III tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu 2024. Mun tabbatar da cewa ba a bar wata al’umma a baya ba; wannan yunƙurin da aka yi ya ba da gudunmawa sosai wajen ganin jiharmu ta samu gagarumar kima a idon Bankin Duniya saboda bajintar da muka yi wajen aiwatar da shirin.”
Bugu da ƙari, Gwamna Lawal ya jaddada cewa bangaren miƙa kufi na shirin yana da nau’i huɗu. “Na farko shi ne tsarin samar da ayyukan yi ga al’umma, wanda duk wanda ya ci gajiyar shirin zai riƙa karbar Naira 20,000 duk wata a tsawon shekara ɗaya.
“Domin tabbatar da daidaito, kashi 60 na wannan kason an ware shi ne ga mata, yayin da sauran kashi 40 na maza ne.
“Kashi 60 ɗin na mata zai shafi matan da mazansu suka mutu, waɗanda aka kashe, da kuma ma’aikatan asibitin sa kai waɗanda ke hidima ba tare da albashi ba.
“Yayin da ake amfani da rajistar zamantakewa, sarakunanmu masu daraja za su taka muhimmiyar rawa wajen zaƙulo wafanda suka cancanta daga al’ummominsu.
“Kashi na biyu kuma shi ne na ‘Social Transfers’, inda za a riƙa bayar da Naira 10,000 duk wata na tsawon shekara faɗa ga bangaren nakasassu, marasa lafiya da kuma tsofaffi.
“Wannan tallafin an yi niyya ne don sauƙaƙe nauyi a kan waɗanda ke fuskantar ƙalubale yau da kullum da kuma tabbatar da cewa za su iya rayuwa cikin mutunci da kwanciyar hankali.
“Tallafin Rayuwa na biyan Naira 150,000 zai dunfari masu ƙananan sana’o’i ne.
“An yi la’akari daidai wa daida ga maza da mata, wanda ake so ya ƙara bunƙasa sa’o’in al’umma. Tun daga samarwa zuwa sayarwa, wannan yunƙuri na da niyyar farfaɗo da ƙananan sana’o’i da haifar da tasirin ci gaban tattalin arziki a cikin al’ummominmu.
“Hakazalika, tallafin Naira 50,000 wnada za a biya a lokaci ɗaya zai shafi ƙungiyoyin da aka yi niyya, waɗanda suka haɗa da ’Yan Agaji, gidajen mata, da kuma malamai na Makarantun Allo da Islamiyya. An tsara wannan matakin ne don ƙarfafa sassa daban-daban na jama’a da kuma ƙarfafa tushen tattalin arzikin yankinmu.”
Gwamnan ya yaba wa kwamitin gudanarwa na NG-CARES da sassan aiwatarwa bisa jajircewarsu wajen ganin an samu sakamakon da ake buƙata.