Home / Labarai / Gwamna Matawalle Ya Nada Sabon Sarkin Kauran Namoda

Gwamna Matawalle Ya Nada Sabon Sarkin Kauran Namoda

Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Mohammed ( Matawallen Maradun) MON, ya tabbatar da nadin Alhaji Sanusi Mohammed a matsayin sabon Sarkin Kauran Namoda.
 Amincewa ta biyo bayan irin shawarar da majalisar zaben Sarki a masarautar Kauran Namoda ta bayar ne kamar yadda yake kunshe a cikin kundin tsarin dokokin masarautar.
Alhaji Sanusi Mohammed ya Gaji tsohon Sarkin ne Alhaji Mohammed Ahmed Asha wanda ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.
Ga hoton sabon sarkin kauaran Namoda a Jihar Zamfara yana cikin kakin soja
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Zailani Bappa, mai ba Gwamnan Zamfara shawara a kan harkokin wayar da kan jama’a da kuma kafafen yada labarai.
Kafin nadin nasa dan shekaru 40 Alhaji Sanusi Mohammed yana aiki da rundunar sojan Nijeriya ne a matsayin Mejo.
 Yayin da Gwamnan yake yin addu’ar Allah jikan mamacin wato tsohon sarki, Gwamna Matawalle ya kuma yi wa sabon Sarkin matan samun nasara a lokacin Mulkinsa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.