Home / Uncategorized / Gwamna Uba Sani Ne Mafita A Jihar Kaduna – Amos Gwamna Magaji

Gwamna Uba Sani Ne Mafita A Jihar Kaduna – Amos Gwamna Magaji

 

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar kananan hukumomin Zangon Kataf Da Jaba dagà Jihar Kaduna Amos Gwamna Magaji, ya bayyana irin salon mulkin Gwamnan Jihar Kaduna Kwamared Sanata  Uba Sani a matsayin hanya mafita a jihar.
Honarabil Amos Gwamna Magaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai Jim kadan bayan karbar lambar karramawar da Kamfanin jaridar “Authentic News Daily” ya yi masa a Kaduna.
“Hakika irin yadda Gwamna Sanata Uba sani ke kokarin rungumar jama’a ta hanyar aiwatar da ayyukan raya kasa da kuma na mutunta dukkan al’ummar jihar Kaduna ya sa jama’ar yankin kudancin Kaduna suka rungumi tafiyar Gwamna Uba Sani da gaskiya da amana”.
Honarabul Amos ya ci gaba da cewa, “sakamakon kokarin Uba Sani ne ya sa ni kaina na koma tafiyar Gwamnati wato cikin APC wanda udan ba haka ba ta yaya za a yi ni in koma wani wuri a siyasa sabanin abin da jama’a ke bukata, ai da sai jama’a sun rika jifana, amma da yake a yanzu salon mulkin siyasar Uba Sani na tafiya da jama’a kowa na gamsuwa sai ga shi ana tafiya tare da kowa cikin martaba da mutuntawa”.
A game da ko zai yi takarar kujerar Dan majalisar dattawa domin wakiltar yankin Kidancin Kaduna kuwa sai Honarabul Amos Magaji ya ce duk wannan lamarin na Allah ne, amma shi abin da ke gabansa shi ne yi wa jama’a aiki kowa ya gani a kasa, wanda kuma babu tababa duk inda aka je jama’a za su shaida irin wakilci nagari da yake aiwatarwa musamman a kananan hukumomin Zangon Kataf Da Jaba, jama’a na murna da farin cikin gani na a matsayin wakilinsu a majalisa.
“Saboda haka mafita shi ne Gwamna Uba Sani a jihar Kaduna musamman irin yadda yake tafiyar da salon mulkinsa.

About andiya

Check Also

Niger Courts Dangote Group’s Partnership To Unlock Crude Oil Potentials

  With its proven expertise in the energy sector, the Dangote Group is well-positioned to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.