Home / Labarai / Gwamna Uba Sani Ya Bayar Da Umarnin Kamo Wadanda Suka Kashe Mutane A Ikara

Gwamna Uba Sani Ya Bayar Da Umarnin Kamo Wadanda Suka Kashe Mutane A Ikara

…Zamu Hukunta Duk Mai Hannu A Kisan

Daga Imrana Abdullahi

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya umurci jami’an tsaro da su binciki kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa musulmi masu ibada a wani masallaci da ke karamar hukumar Ikara a jihar, ya kuma bukaci jami’an da su farauto wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

Gwamnan a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai Muhammad Lawal Shehu ya fitar, ya bayyana lamarin a matsayin mugunta da dabbanci da aka ruwaito na kashe masu ibada a wani Masallaci.

“Don haka ya umarci jami’an tsaro da su binciki lamarin sosai tare da bin diddigin wadanda suka aikata laifin.”

Gwamnan da ya fusata ya sha alwashin cewa zai bi  duk wani mataki da doka ta dauka na ganin an hukunta barayin Ikara.

Ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane bangare na jihar ta Kaduna.

“Mun fahimci damuwa da damuwar mazauna Ikara musamman da jihar Kaduna gaba daya.  Amincin ku da tsaron ku su ne manyan abubuwan da muka sa a gaba, kuma muna so mu tabbatar muku da cewa muna aiki tukuru don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

“Muna karfafa wa jama’a gwiwa da su kwantar da hankula da kuma lura a wannan lokacin.  Muna kuma kira ga dukkan mazauna garin da su ba jami’an tsaro hadin kai tare da bayar da duk wani bayani da ya dace da zai taimaka wajen binciken da ake yi.”

Gwamnan ya kuma aika da tawaga karkashin jagorancin Malam Samuel Aruwan, mai kula da ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida domin jajantawa al’ummar kauyen Saya-Saya da ke karamar hukumar Ikara, inda lamarin ya faru.

Tawagar za ta kuma gudanar da aikin tantance yanayin tsaro da jin kai a yankin da kuma ba da shawara ga gwamnati.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.