Home / Big News / Gwamna Uba Sani Ya Raba Wa Masu Bukata Ta Musamman Filaye A Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Raba Wa Masu Bukata Ta Musamman Filaye A Kaduna

Daga Imrana Abdullahi
.Dokta Bashir Garba Ibrahim Darkta Janar ne a Hukumar da ke Kula da al’amuran Filaye a Jihar Kaduna “KADGIS” ya bayyana cewa Babban dalilin da ya sa ya bayar da Takardun mallakar Filaye GA masu bukata ta musamman a Jihar Sakamakon Umarni ne da Gwamna Kwamared Sanata Una Sani ya bayar da nufin sakama masu bisa irin gudunmawar da suka bayar a lokacin ana Neman zabe da kuma lokacin da aka gudanar da zabe har Gwamna Uba Sani ya samu nasarar da aka samu darewa a Kan kujerar Gwamnan Jihar Kaduna.
Dokta Bashir Garba Ibrahim Darkta Janar na hukumar Kula da al’amuran Filaye ya bayyana hakan ne a lokacin da ya Kira Manema labarai a ofishinsa cikin garin Kaduna inda ya mikawa masu bukata ta musamman Takardun filayen.
” A bisa wannan tsarin ne aka sa mu Neman wadannan mutane masu bukata ta musamman kuma bayan sun zo aka Gayawa Gwamna ga su sun zo sai Gwamna ya bayar da Umarni lallai a ba su wadannan Takardun filaye, kuma a yau mun Kira su mun kuma ba su wadannan Takardun filayen cewa GA sakon da Gwamna ya ce a ba su domin irin gudunmawar da suka bayar tun a lokacin Neman zabe, Shi ya sa aka fara saka masu domin su ci guminsu na Siyasa. Kuma da akwai wadansu kungiyoyin da yawa da Gwamna ya bayar da Umarni a kyautata masu kuma muna binsu daya bayan daya.
Dokta Bashir ya Kara da fayyace cewa, ” ba a taba samun Gwannatin da take bayar da Filaye kamar wannan Gwannatin da Sanata Una Sani ke yi wa Jagoranci ba, da akwai mutane da yawa da suka taimaka har da wadanda ma ba su taimaka BA duk an taimake su kuma da yardar Allah za mu ci gaba da taimakawa Jama’a domin Gwamna ya bayar da Umarni a taimakawa al’umma kuma za a yi taimakon”.
Sai dai Dokta Bashir Garba Ibrahim ya shaidawa Manema labarai cewa wadanda aka ba Takardun filayen nan da ke da bukata ta musamman sun Kai mutane Talatin (30) da suke a wurare daban daban.
.Da Yake tofa albarkacin bakinsa bayan sun karbi Takardun Salisu Isa da ke da Zama a karamar hukumar Kaduna ta Arewa kuma Mataimakin shugaban a kungiyar masu bukata ta musamman da ke a yankin Kaduna ta tsakiya, wato ( Kaduna central disable development association) da suke goyon bayan Gwamna Uba Sani dubu bisa dubu ba wai dari bisa dari ba.
Ya ce Babban dalilin da yasa a duk inda Gwamna Malam UBA Sani Yake suke Kai Kai su wurin Shi ne domin su a iya saninsu ba a taba yin Gwamnan da ya daraja nakasassu ba kamar SA da yake ba mu aiki da abin yi kamar UBA Sani ba.
” Dalilin zuwan su wannan wuri na ofishin hukumar Kula da al’amuran Filaye ta KADGIS Shi ne tun da suke a Jihar Kaduna kasancewarsu na haifaffun Yan Jihar Kaduna,Amma ba a taba ba su wurin Zama da za a ce mun mallake Shi ba na mu ne mu zauna da iyalan mu sai a wannan Gwannatin ta Uba Sani da ta Saba taimakon Jama’a. Sai muka ce Muma fa mutanen Uba Sani ne da ya San mu tun kafin ya Zama Gwamna za mu roki Dokta Bashir a Gaya wa Gwamna Wanda a yanzu Gwamnan ya sa aka taimake mu dari bisa dari, an ba mu Filaye an ce kowa ya je ya zauna da iyalinsa, kuma da ikon Allah a cikin kungiyar mu ba Wanda zai sayar da filinsa kowa Gina wa zai yi ya zauna”.
“Muna yin wa Darakta Janar na hukumar KADGIS godiya mara misaltuwa domin ya yi mana kokarin kwarai da gaske saboda mun Sha Neman taimako a can baya Amma BA a yi mana ba sai Shi a yanzu ya Kai wa Mai girma Gwamna kukan mu domin a taimake mu kuma ya taimake mu, muna godiya kwarai.

About andiya

Check Also

Dangote headlines 2026 Gateway Trade Fair as Gov Abiodun hails Group for boosting Ogun’s Industrial Competitiveness

Ogun State Government has lauded the roles being played by the Pan-Africa conglomerate, Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.