Home / Ilimi / Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Likita Bayerabe  Da Miliyan 13.9, Motar Hawa

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Likita Bayerabe  Da Miliyan 13.9, Motar Hawa

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Likita Bayerabe  Da Miliyan 13.9, Motar Hawa
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya amince da a biya kudi naira miliyan 13.9 tare da bayar da motar hawa a matsayin kyauta ga wani Likita mai shekaru 65 daga Jihar Ogun.
Shi dai wannan Likitan ya zauna ne a garin Manguno a babban asibitin Gwamnati kuma ya zauna yana ta duba marasa lafiya koda garin na fama da matsalar Yan Boko Haram a yan shekarun da suka gabata.
Dokta Isa Akinbode, dan asalin Jihar Ogun ya kammala karatun Digirinsa ne a jami’ar Maiduguri ya kuma shiga aikin Jihar Borno ne inda ya yi aiki tsawon shekaru 22 kafin ya ajiye aiki a shekarar 2016 daga babban asibitin Manguno.
Bayan ajiye aiki, Likitan duk da cewa akwai rahotannin cewa an ta ba kama shi amma daga baya yan kungiyar Boko Haram sun sake shi a Manguno, kuma ya ci gaba da gudanar da aikin duba marasa lafiya a babban asibitin Manguno a matsayin mai aikin sa kai domin jin kan jama’a.
Amma Gwamna Kashim Shetima, lokacin da ya kawo wata ziyarar aiki a Manguno, ya bayar da umarni ga manyan ma’aikatan ma’aikatar lafiya ta Jihar Jihar su ba Dokta Akinbode aikin kwantaragi.
Sakamakon irin yadda aikin wadansu manyan jami’an ma’aikatar lafiya ya faru na yin kirkiri  tabbatarwa da Likitan aikin da za a bashi na Kwantaragi, amma duk da hakan Likitan ya ci gaba da aikinsa.
Shekaru biyar bayan nan, Gwamna Zulum a ranar Juma’a ya bayar da umarnin cewa a biya shi dukkan kudin da ya dace a matsayin bashin da yake bi na ariya daga shekarar 2016. Gwamnan ya kuma bayar da umarnin cewa a ci gaba da biyansa kudin kwantiragin wata wata.
Gwamnan ya kuma mika wa Likitan mota kirar Tayota Highlander a matsayin kyauta ga Dokta Akinbode a matsayin sakamakon aikin da ya yi wa mutanen Jihar Borno.
“Mutane irinsu Likita Akinbode mutane ne da ya dace a karfafa masu Gwiwa, ya zauna a Manguno duk da irin matsalar tsaron da ake fama da ita.
Wanda na gada a lokacin da ya kawo ziyara Manguno,ya bayar da umarnin cewa a bashi aikin Kwantaragi, amma saboda matsalolin gudanar da aikin Gwamnati ba a samu damar aiwatar da umarnin ba. Amma a yanzu na yanke hukunci in sake bashi aikin kwantaragi.
Muna biyan dukkan harkokin albashinsa ina bashi takardar cire kudi ta Banki domin ya samu kudi naira miliyan 13.9. Kuma na amince da sake daukarsa tun daga shekarar 2016 ranar da ya ajiye aiki”, Inji Zulum.
Gwamna Zulum ya kuma amince da daukar Dokta Akinbode yar Likitan, da ta karanci harkokin mulki a jami’ar Maiduguri, an dai ba ta aikin ne a matsayin ma’aikaciyar Gwamnatin Jihar Borno.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.