Home / Labarai / Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Rabon Kudi Biliyan 1

Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Rabon Kudi Biliyan 1

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Barno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum ta ware kudi naira biliyan daya domin taimakawa kananan masu sana’a ta yadda za su samu bunkasa.
Babagana Zulum wajen kaddamar da wadannan makudan kudi biliyan daya ya bayyana kashe bangar siyasa inda ya yi gargadi a kan samar da yan bangar siyasa da ke haihuwar yan Ta’adda a cikin al’umma.
A wannan hoton za a iya ganin wani daga cikin Maza da suka amfana da kudin

Gwamnatin Jihar Borno tare da hadin Gwiwar Bankin masana’antu na tarayya suka hada Gwiwa wajen samar da kudi naira biliyan daya domin bayar da bashi mara ruwa ga masu kanana da matsakaitan masana’antu, inda kowane bangare ya samar da kudi naira miliyan dari biyar (500) miliyan.

Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya kaddamar da kashi na biyu domin bayar da tallafin inganta tattalin arzikin jama’a musamman masu kanana da matsakaitan  sana’a’o’i a kananan hukumomi shida.
Makudan kudi naira biliyan daya ne aka ware domin rabawa masu sana’a guda dubu 5,000 daga kananan hukumomi guda shida da suka hada da Biu,Gowza,Ngala,Monguno,Mobbar da cikin birnin Maiduguri.
An kuma raba sama da motoci 80 da suka hada da Keke Napep da wadansu suka samu amfana domin Tallafawa rayuwarsu su samu abin da za su rika rayuwa da shi na yau da kullum.
A cikin watan Disamba 2019, an raba kudi naira miliyan dari 384 domin rabawa masu yin bara a kan tituna sai kuma a watan Janairu 2020, an raba kudi naira miliyan dari biyar da sha biyar (515) a wani shirin yin aiki domin a amfana tsarin da mutane dubu biyu da dari Takwas da sittin da biyu (2,862) da aka rika ba yan bangar siyasa da ake kira “Ecomog”, suka amfana da kudi naira dubu Talatin kowane wata har na tsawon rabin shekara. Matasan na karbar kudi duk wata bayan da suka rika yin aikin share tituna. A watan Disamba 2020, an rabawa masu sana’o’i daban daban kudi naira miliyan 154 a Maiduguri.
Wasu daga cikin motocin da Gwamna Zulum ya rabawa jama’a.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Zulum ya bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da abin da aka ba su kamar yadda ya dace.
A wani ci gaban da aka samu kuma Gwamna Babagana Umara Zulum, ya kara tsawon wurin da hanin da ya yi a kan bangar siyasa zuwa Biu.
Gwamna Babagana Umara Zulum kenan tare da sauran jama’a a wurin taron rabon kudi, motocin hawa da Keke Napep masu kafa uku
Inda Gwamnan ya bayar da umarni ga dukkan hukumomin tsaro da su kama duk wani ko wata da ke bayyana kansa ko kanta a matsayin dan bangar siyasa da suke yi wa jama’a Ta’adda.
“Kwamishinan yan Sanda, Daraktan yan Sandan farin kaya, da dukkan hukumomin tsaro tuni aka ba su umarnin kama duk wani mai kiran kansa da ECOMOG daga karfe shida (6) na safiyar gobe”.
Ya kuma ce, “duk wani dan siyasar da ke daukar nauyin wadannan masu bangar siyasa zai dandana kudarsa”. Inji Zulum.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.