Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan jihar Binuwe, Rabaran Fada Hyacinth Alia ya jinjinawa wanda ya kafa gamayyar jami’on Maryam Abacha American University a Nijeriya da Nijer, Franco-British International a Kaduna da Canadian University a Abuja, Farfesa Adamu Gwarzo kan yadda yake nuna kishin ci gaban ilimi a Nijeriya da ma Afrika baki daya a aikace.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara ta musamman da ya kai wa Jami’ar Maryam Abacha American University dake Kano a ranar Lahadi 11 ga watan Fabarairun 2024 a daidai lokacin da yake ganawa da ‘yan kabilar Tiv mazauna garin Kano a cikin Jami’ar ta Maryam Abacha American University a Kano.
Gwamnan ya fara ne da jinjinawa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo wanda ya bayyana a matsayin “matashin Farfesa”. Inda kuma ya ce Farfesa Gwarzo mutum ne mai son ganin ci gaban ilimi. Kuma mutum ne mai jin kan talakawa da wadanda ba su da shi; “mutum ne mai son sha’anin ilimi sosan gaske. Mutum ne wanda zuciyarsa take jin kan talakawa da wadanda ba su da shi. Mutum ne wanda ya nuna cewa idan Allah ya albarkace ka kaima ka albarkaci wasu”, ya nusasshe.
Ya ci gaba da cewa; “akwai ‘yan asalin jihar Binuwe da dama da suke aiki a wannan jami’a. Ba kawai a nan ba, har ma da sauran ire-iren wadannan jami’o’in na shi a Abuja da kuma Kaduna da kuma jamhuriyyar kasar Nijer”, ya lurantar.
Gwamnan ya ce ya yi matukar jindadi dangane da shaidar da Farfesa Gwarzo ya bayar dangane da yadda ya yi aiki cikin gaskiya da rikon amana da ‘yan asalin jihar Binuwe. “shi mutum ne wanda ya kasance abokin mutanen Binuwe. Shi amintaccen aboki ne. Kuma mutum ne wanda ya damu matuka da ci gaban jihar Binuwe.
Farfesa Gwarzo a na shi jawabin, ya yi wa jihar Binuwe fatan alheri. Inda ya ce sun yi sa’ar samun natsattsen mutum a matsayin gwamna. Inda ya ce “nan ba da jimawa ba talauci zai yi kaura daga jihar Binuwe. Za a samu matasan masu kudi a Binuwe.
Ya ce yanzu duk wanda ya je Binuwe zai samu jihar ba kamar yadda ya santa ba. “jihar Binuwe ta yanzu jiha ce ta aiki. Ba jihar yada kiyayya da gaba ba”.
Sannan Farfesa Gwarzo ya ce yana da dimbin ma’aikata ‘yan asalin jihar Binuwe wanda ya yi aiki da su, kuma tabbas ya ji dadin aiki da su. “Na yi aiki da ‘yan asalin jihar Binuwe da dama, na ji dadin aiki da su, mutane ne masu gaskiya da kamala”, Farfesa Gwarzo ya jaddada.
Farfesa Gwarzo ya ce kofarsa a bude take ga mutanen jihar Binuwe, duk abin da suke so su tuntube shi kawai kai tsaye.
A karshe ya zagaya da gwamnan sassa daban-daban na Jami’ar.