Daga Imrana Abdullahi
Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina ya amince da nadin Abba Dayyabu Safana da Abba Zayyana a matsayin sabbin manyan manajojin gidan rediyo da talabijin na jihar.
Hakazalika, Gwamna Dikko Umaru Radda ya kuma amince da nadin Shafi’u Abdullahi a matsayin sabon Babban Darakta na Hukumar Laburare ta Jihar.
Haka kuma Gwamna Radda ya amince da nadin Dakta Salisu Abdullahi a matsayin Darakta-Hukumar Ilimin Musulunci ta Jiha.
Gwamna Dikko Radda a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, ya bukaci sabbin wadanda aka nada da su kasance masu himma tare da kokarin ganin jihar ta samu daukaka.
Gwamnan ya bada tabbacin cewa, kofofin sa a bude suke a koda yaushe ga duk wani sabon tunani da zai ciyar da jihar gaba