Home / Labarai / GWAMNATI TA SAKE DUBA TSARIN CANZA FASALIN KUDI – DOKTA SULEIMAN

GWAMNATI TA SAKE DUBA TSARIN CANZA FASALIN KUDI – DOKTA SULEIMAN

DAGA IMRANA ABDULLAHI

An bukaci Gwamnatin tarayya ta hannun Gwamnan babban Bankin Najeriya da ta sake duba irin yadda ake aiwatar da batun canza Fasalin kudi a duk fadin kasar baki daya.

Amir na kungiyar habbaka al’amuran addinin Islama ta (MICA) Dokta Suleiman ne ya yi wannan kiran lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron Lacca da kungiyar ta saba yi duk shekara a watan Ramadana.

Dokta Suleiman ya ci gaba da bayanin cewa “hakika tsarin sake Fasalin kudi abu ne mai kyau, amma duk da hakan ya dace babban Bankin Najeriya ya sake duba tsarin domin a samu ingantaccen tsari mai cike da tausayawa al’ummar kasa baki daya”.

“Hakika batun samun takardun sababbin kudin da aka sakewa fasali ya haifarwa jama’a wadansu dimbin matsaloli da yawa, har ina ganin kamar mutane ba su taba shiga wahala ba kamar yadda suka shiga sakamakon kokarin canjin sababbin  kudin da Gwamnati ta samar ba”.

Saboda haka ne muke son Gwannati ta sake duba wannan tsarin musamman a duk inda yake da matsala ga jama’a. Kuma ya dace idan za a aiwatar da tsarin a bayar da wadataccen lokaci sosai, shin wai me yasa aka kirkiri hukumar wayar da kawunan jama’a ta kasa (NOA) ai domin fadakar da jama’a ne a dukkan birane da karkatar kasa kuma za a iya aiwatar da wannan fadakarwa koda kuwa a wasu yaruka da ake amfani da du ne a kasar domin kowa ya fahimci abin da ake nufi, kafin shigowa da tsarin cikin jama’a. Amma sakamakon rashin fadakarwa sosai kamar yadda ya dace a game da tsarin ya haifarwa mutane matsananciyar wahala kwarai, kuma ba wai tsarin bashi da kyau ba ne baki daya.

“Kuma mu ba muna kalubalantar tsarin ba ne, a a mun dai ga ya dace a samu tsarin tausayawa jama’a wajen aiwatar da tsarin baki daya.

Dokta Suleiman ya lissafa irin ayyukan da kungiyar ( MICA) ke aiwatarwa da suka hada da yin taron bita domin fadakar da jama’a, yin tafsir a dandalin Sada zumunta na zamani, yin wa’azi a watan Azumin Ramadana da harshen Turanci, da kuma tattara sababbi da tsofaffin Suturun da jama’a suka taimaka da su da ake bayarwa taimako ga wasu sai kuma taron mata domin tattaunawa a kan al’amuran yau da kullum a tsakaninsu da dai sauran ayyuka da dama domin inganta rayuwar bil’adama.

Da yake nasa jawabin babban bakon da ya gabatar da lacca a wajen taron Dokta Muhammad Kabir Muhammad, babban jami’i a Bankin TAJ da ke Abuja.

Inda ya ce abin da ya gabatar a wajen laccar ta kungiyar MICA, a shekarar 2023 shi ne ta mayar da hankali ne a game da ainihin batun sake Fasalin kudin da Gwamnatin tarayya ta yi da kuma abin da lamarin ya haifar musamman a kan tsarin Babban Bankin kasa da ya shafi daukacin yan Najeriya.

A game da batun tsarin da babu kudin ruwa a ciki hakika akwai shimfidaddun dokokin da ya dace a aiwatar da wadanda ba za a aiwatar ba.

Saboda a karkashin tsarin shari’ar Islama kudi ba wani kayan Sayarwa ba ne ko kuma a sayo daga wani wuri.

“Saboda haka ne wadanda suka rika sayar da kudi ga jama’a a lokacin wahalar da aka shiga kwanan baya ta rashin wadatattun kudi, hakika abin da suka yi ya sabawa shari’ar musulunci, musamman idan an zo ga batun yadda ake harkar kudi a tsarin Islama duk bai amince da wannan aikin ba.

Wato abin da ake nufi da kudi shi ne abin da duk kowace al’umma ta bayyana a matsayin kudi don haka ko a tsarin shari’a duk abin da wata al’umma ta ga ya dace ya zama matsayin kudi wannan shi ne kudi.Ko kudi a yanar Gizo ko kuma tsabar kudi a fili da za a iya gani a kuma taba da hannu ayi amfani da shi.

“Don haka tsarin sake Fasalin kudin da Gwannati ta yi duk shari’a ta amince da hakan duk musulmi za su iya yin amfani da su wajen karbar kudin da aka biya su ko kuma biyan bashi.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.