Home / Labarai / Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Karyata Batun Kacaccala Masarautar Zazzau Gida Uku

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Karyata Batun Kacaccala Masarautar Zazzau Gida Uku

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Karyata Batun Kacaccala Masarautar Zazzau Gida Uku

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El – Rufa’i, ta Karyata jita jitar da ake yadawa cewa wai Gwamnatin na son kirkiro wadansu sababbin Masarautu huda uku a cikin masarautar Zazzau.
Kwamishinan kula da tsaro harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a Kaduna.
Kwamishina Samuel Aruwan ya bayyana cewa babu wani batun shirin aikewa majalisa da wani kudirin doka daga bangaren Zartaswa kamar yadda wadansu mutane ke yada kanzon Kurege ba gaira ba dalili.
“Wadansu mutane ne kawai da suka kware wajen kirkirar jita jita domin neman haddasa fitina kawai, babu wata magana ko shiri mai kama da hakan saboda masarautar Zazzau na da dimbin tarihi kuma babbar masarauta ce da ke da matukar muhimmanci kwarai”.
Ya ci gaba da cewa Gwamnati dai na yin aiki ne tare da doka da bin tsarin da dokar ta tanadar don haka a nan bada jimawa ba za a bayyana sunan sabon Sarkin da Allah ya ba Sarautar Sarkin Zazzau.
Jama’a su kwantar da hankalinsu kada su yarda wani ya rudar da su a tayar da fitina.
Labarai dai sun cika kafafen yada labaran yanar Gizo da kuma jaridu cewa ana shirin aikewa da majalisar dokoki kudirin Kacaccala masarautar Zazzau zuwa gida uku wato masarautar Birnin Kaduna, Zazzau da kuma ta Kudan, amma da wannan bayani na Samuel Aruwan ta tabbatar duk labaran da ake yadawa ba su da tushe balantana makama.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.