Home / Labarai / Rundunar Yan sandan Jihar Kano Ta Kama Matar da Ta Kashe Yayan Cikinta Biyu

Rundunar Yan sandan Jihar Kano Ta Kama Matar da Ta Kashe Yayan Cikinta Biyu

Rundunar Yan sandan Jihar Kano Ta Kama Matar da Ta Kashe Yayan Cikinta Biyu
Imrana Abdullahi
Rundunar yan sandan Jihar Kano karkashin jagorancin Kwamishina Habu A Sani, Psc ta bayyanawa daukacin al’umma cewa ta kama matar da ta kashe yayan cikinta biyu mace da Namiji
Matar mai suna Hauwa Habibu yar shekaru 26, da ke zaune a unguwar Diso cikin birnin Kano karamar hukumar Gwale
Kamar yadda sanarwar Rundunar yan sandan ta bayyana wadda ke dauke da sa hannun mai magana da yawunsu Abdullahi Haruna ta ce yaran masu suna Irfan Ibrahim mai shekaru 6 da Zuhura Ibrahim Ibrahim shekaru 3, mahaifiyar tasu ta kai wa yaran hari ta kuma kashe su ta kuma raunata wata yarinya mai suna A’Isha Sadiq mai shekaru 10 wadda suna zaune ne a kusa da su amma nan da nan ta Tsere zuwa wani wuri inda ta biye.
A lokacin da jami’an tsaron sula samu labarin nan da nan suka yi hanzari zuwa wajen sai suka dauki wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Gwamnatin Jihar Kano na Murtala Muhammad a cikin birnin Kano inda Likita ya tabbatar da mutuwar yaran, an kuma ce an dauke A’Isha Sadiq an mayar da ita zuwa asibitin kwararru na Malam Aminu Kano da le Kano inda aka duba lafiyarta aka kuma sallameta.
Kwamishinan yan sandan na Jihar Kano Habu A Sani Psc ya bayar da umarni ga babban baturen yan sanda DPO mai kula da Ofishin yan sanda da ke Gwale SP Nasiru Gusau da su kamo wadda ta aikata laifin cikin awa 24 an kuma yi nasarar kama ta a ranar.
Abin da binciken farko ya bayyana cewa wadda ake zargin ta tabbatar da cewa ta kulle gidan ta kuma yi amfani da Adda da kuma wani makamin da aka yi da alminion ta kaiwa yaran guda uku hari abin da yasa suka samu raunuka a wurare daban daban na jikinsu inda sakamakon kokarin da jami’an yan sanda suka yi cikin Sauri aka samu nasarar tsira da ran A’Isha wadda ta bayar da mummunan labari mara dadin ji yadda lamarin ya faru.
Kwamishinan yan sanda Habu A. Sani, psc davale wa lakabi da magana daya (Kalamu-Waheed) ya bayar da umarnin a mayar da batun kisan zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar domin ci gaba da bincike.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.