….Minista Bello Matawalle na daukar mataki a koda yaushe
Daga Imrana Abdullahi
An kira ga daukacin Gwamnonin arewacin Najeriya da su yi ko yi da irin salon Gwamnan Jihar Kaduna wajen maganin matsalar tsaron da ke damun al’umma Dare da Rana.
Wani tsohon mai ba tsohon Gwamnan Jihar Zamfara shawara kuma a halin yanzu ministan kasa a ma’aikatar tsaro Dokta Muhammad Bello Matawalle shawara a kan harkokin hulda da kasashen waje da kuma kulla yarjeniyoyi Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya yi wannan kiran a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Dokta Suleiman Shinkafi ya ci gaba da fadakarwa ga Gwamnonin daukacin arewacin Najeriya cewa yin sulhu da kuma daukar duk wata hanyar da za ta kawo karshen irin tashe tashen hankalin rashin tsaron da ake fama da shi ne kawai mafita.
Saboda, ” ana ta kashe jama’a Dare da rana safiya da maraice jama’ar yankin arewacin Najeriya ba su da zaman lafiya kullum suna cikin halin tsoro da rashin kwanciyar hankali, kuma ba su da makaman da barayi da yan Ta’adda suke da su a cikin Daji, don haka lallai ya zama wajibi ayi sulhu da bin duk wata hanyar kawo karshe lamarin”.
Dokta Shinkafi ya kara da cewa suna yin godiya kwarai da ministan kasa a ma’aikatar tsaro Dokta Bello Matawalle bisa irin yadda yake fada dacikawa a game da wannan harka ta yan Ta’adda.
“Tun da na shaida masa irin hali na yanayin da jama’ar Shinkafi ke ciki nan da nan sai ga shi sojojin Najeriya sun shiga aiki suna dajin Shinkafi suna ta aiki kuma a yanzu jama’a da dama suna ta kira na a waya suna godiya domin hakika sojoji sun shiga aikin tabbatar da tsaro gadan gadan ba tare da bata lokaci ba”, inji Dokta suleiman Shinkafi.
“Mun samu labarin tuni aka tarwatsa wurin da Turji ke ajiye abinci a wata makaranta an kuma kai masa hari har ana ganin lallai ya ruga da rauni a jikinsa kuma an yi maganin wadansu makusantansa domin tuni kamar yadda muke samun labari sun bakunci lahira”. Inji Dokta suleiman Shinkafi.
” Mun kuma samu labarin an yi abin da ba a taba yi ba a garin Shinkafi da wadansu wurare domin jami’an tsaro sun kama wadansu manyan mutane a Shinkafi da wannan yankin da ba a ta ba yin hakan da domin ana zargin su da hannu a lamarin yan Ta’adda na bayar da bayanai”, inji Suleiman Shu’aibu Shinkafi.
Kuma muna kara yin kira ga jama’a da si ci gaba da bayar da muhimmanci a kan yin addu’o’in Dare da rana safiya da maraice da nufin kawo karshe wannan lamarin kuma Allah ya kara Dora jami’an tsaro a kan wadannan mutane ya bindiga.
” muna kara yin godiya ga ministan kasa a ma’aikatar tsaro Dokta Bello Muhammad Matawalle a kan irin yadda yake hanzarta daukar matakan da suka dace, kuma ya dace jama’a su Sani cewa shi ministan tsaro rundunar tsaron sojoji ta ruwa ce da wadansu bangarori ke karkashin sa kuma wadannan yan Ta’adda da suke a cikin daji ba acikin ruwa suke ba amma duk da haka ministan kasa na saurin hada kai tare da ministan Tsaro Badaru Abubakar domin daukar matakan da ya dace a kawo karshe matsalar don haka muka yaba masu baki daya da dukkan shugabannin rundunonin tsaron sojan kasa, na Sama da na ruwa irin yadda suma suke gudanar da aiki ba tare da gajiyawa ba”.
” a fa duba irin yadda matsalar nan ta kasance a yankin Jihohin Katsina, Zamfara da Sakkwato don haka daukar mataki irin na Gwamnan Jihar Kaduna na da matukar muhimmanci kwarai ta yadda jama’a za su samu maslaha. Saboda yan bindigar nan na da fa makamai manya kuma.masu yawa