Home / Labarai / Gwamnonin Arewa Sun Yi Watsi Da Bukatun Gwamnonin Kudancin Najeriya

Gwamnonin Arewa Sun Yi Watsi Da Bukatun Gwamnonin Kudancin Najeriya

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnonin arewacin Najeriya Goma sha tara (19) sun bayyana yin watsi da bukatun da suke kokarin neman wai sai a ba su damar samar da shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Gwamnonin na Arewa sun bayyana hakan ne a karshen wani babban taron da suka yi tare da manyan sarakunan yankin na Arewa taron dai sun yi shi ne a babban dakin taro na gidan Gwamnatin Jihar Kaduna.
Gwamnonin karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Filato Samuel Bako Lalong, inda suka bayyana cewa bukatar da Gwamnonin na Kudu suka bayyana cewa wai sai a ba su shugabancin kasar nan a matsayin abin da ya sabawa dokar kasa domin ba wanda ya hana kowa tsayawa takara a zabe shi bisa dokar kasa.
Don haka suka ce su ba su tare da wannan bukatar da wasu ke cewa sai a ba su shugabanci haka kawai bayan ga tanajin da tsarin Dimokuradiyya ya yi.
A game da turka turkar da ake yi game da batun karbar harajin kayayyaki kuwa, Gwamnonin sun bayyana cewa su duk abin da ake yi su na nan tare da tsarin Gwamnatin tarayya kuma su masu yin biyayya ne ga hukuncin kotu.
Amma ai kayayyakin da ake yi a yankin Arewa ne ake sayar da su, amma wasu kamfanonin sun ajiye hedikwatocinsu ne kawai a Legas amma ana sayar da kayan ne a arewa.
Gwamnonin sun kuma ce suna goyon bayan irin aikin da ake yi na kokarin kawar da yan Ta’adda masu haifarwa jama’a da kasa matsaloli ba gaira ba dalili kawai.
Gwamnonin da Sarakuna sun tattauna a kan abubuwa da dama kuma sun bayyana cewa su na nan a kan tabbatar da ci gaba da samawa yankin ci gaban da ya kamata.
Sarakunan da suka halarci taron sun hada da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abibakar III, Shehun Borno, Sarkin Katsina, San Kano, Sarkin Adamawa, Sarkin Zazzau sai kuma sarakunan sun hada da ONi na Abaji, Ohinoyi na  Ibira, Sarkin  Gumi da Sarkin Fila duk sun halarci taron.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.