Wani hadarin Jirgin ruwan Kwale kwale ya halaka mutane 26 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a kauyen Gbajibo da ke karamar hukumar Mokwa a jihar Neja.
An tattaro cewa, kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji kusan 100 daga kauyukan Gbajibo, Ekwa, da Yan-kede, ya kife ne da safiyar Lahadi tare da mata da kananan yara, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar yawancin wadanda suka jikkata.
Wannan dandali na yanar gizo ya tattaro cewa wani gida a kauyen Yan-kede ya rasa mambobinsa kusan takwas a lamarin.
Da yake tsokaci kan lamarin, gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Bologi Ibrahim ya fitar, ya jajantawa iyalan mamacin.
Bago, yayin da yake nanata mahimmancin amfani da rigunan ceto a lokacin da ake shiga jirgin ruwa ya kuma bukaci jama’a da su daina yin cunkoso a kwale-kwale.
Hakazalika gwamnan ya umurci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja da ta tallafa wa wadanda abin ya shafa a wannan mawuyacin lokacin da ake ciki.
Sanarwar ta kara da cewa, a halin yanzu ana ci gaba da aikin ceto wadanda suka hada da ‘yan sandan ruwa da masu ruwa da tsaki na cikin gida tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja domin neman wadanda suka tsira da rayukansu sakamakon lamarin