Related Articles
Hakika Balarabe Musa Ya Yi Wa Kasa Aiki – Mohammadu Sanusi II
Mustapha Imrana Abdullahi
Mai martaba tsohon Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya bayyana marigayi tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa a matsayin mutumin da ya bautawa kasa baki daya.
Mai martaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar gaisuwar ta’aziyyar marigayin a gidansa da ke Kaduna.
“Hakika marigayin ya bautawa Nijeriya da Jihar Kaduna baki daya don haka rashinsa babban rashi ne ga kasa da al’umma baki daya”.
Ya kara da cewa sati biyu nan baya sun yi magana a waya da marigayin har nake cewa idan na shigo kasar zan zo domin in gaishe shi, to haka Allah ya Kaddara, muna addu’ar Allah ya jikansa da rahama.
Mai martaban ya zo ta’aziyyar ne tare da dukkan tawagar mutanensa baki daya.
Sai tsohon mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro Alhaji Aliyu Muhammad Gusau da tawagarsa duk sun je gidan marigayin domin yi wa iyalai da daukacin Jama’a ta’aziyyar.