Related Articles
Hukumar Babban Birnin Tarayya Ta Haramta Zanga Zanga
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da ke fita daga hukumar babbar birnin tarayyar Abuja na cewa sun haramta Zanga Zangar da ake yi da kuma duk wani nau’in taron jama’a da makamancin hakan a babban birnin tarayyar.
Batun dai zanga Zangar da ake ciki a wadansu Jihohin Nijeriya sun hada da Abuja, kuma ana yin hakan ne sakamakon korafin da jama’a ke yi na uzzurawar da jami’an yan sanda ke yi wa jama’a.