Home / Labarai / Hukumar Kiyaye Hadurra  Za Ta Fara Gagamin Wayar Da Kan Jama’a Na Karshen Shakara A Jihar Kaduna

Hukumar Kiyaye Hadurra  Za Ta Fara Gagamin Wayar Da Kan Jama’a Na Karshen Shakara A Jihar Kaduna

Daga Imrana Abdillahi

 

Kwamandan rundunar hukumar kiyaye hadurra ( FRSC) ta kasa reshen Jihar Kaduna Kabiru Yusuf Nadabo, ya bayyana cewa tuni sun shirya tsaf domin gudanar da gangamin wayar da kan daukacin jama’a game da ayyukan da suke yi musamman a karshen watanni hudu na shekara har zuwa cikin farkon shekara mai zuwa.

 

Shugaban hukumar na Jihar Kafuna, Kabir Yusuf Nadabo ne ya bayyana hakan a taron manema labarai daya ya yi a cibiyar Kungiyar Yan Jarida ta kasa (NUJ), reshen Jihar Kaduna domin isar da sakon cewa a ranar Litinin mai zuwa ne za su yi babban taron gangamin kaddamar da ayyukan wayar da kan da za a yi a babban filin wasa na Ahmadu Bello da ke cikin garin Kaduna.

” hakika za mu yi babban taro a ranar Litinin mai zuwa a garin Kaduna taron kuma zai samu halartar dimbin al’umma daga ko’ina a cikin fadin Jihar Kaduna inda za a fadakar da jama’a game da ayyukan da ake gudanarwa musamman a watanni karshen shekara zuwa cikin farkon shekara mai kamawa”.

A cewarsa, “ana shirya wannan gangamin taron ne a duk shekara-shekara, wanda a yanzu za a yi taron ne domin wayar da kan masu amfani da hanyoyin kan dokokin hanya daban-daban”.

Kwamanda Kabir Nadabo ya kara da cewa yayin taron gangamin wayar da kan jama’a na wannan shekarar zai hada da kungiyoyi daban-daban kamar su NURTW, RTEAN, kungiyoyin mata, da mata yan kasuwa, kungiyoyin farar hula da ‘yan kasuwa masu keke Napep wadanda duk za su halarci taron gangamin”.

Ya kuma umarci masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar da su guji yin ganganci na yin katsalandan a kan dokokin hanya don kiyaye lafiyar jama’a da ta hanyoyinmu.

Kwamandan na  FRSC ya kuma gargadi masu yin tuki da su guji yin gudun wuce sa’a, da daukar nauyin fasinjoji da kuma yin illa ga tsaron titi.

Daga nan sai ya nemi goyon bayan al’ummar Jihar Kaduna ga hukumar FRSC a kokarinta na kare lafiyar jama’a da ayyukan ceto domin tabbatar da zaman lafiyar al’umma Baki daya.

A cewarsa, a ranar Litinin  hukumar ta shirya gudanar da wani taron karrama wasu al’umma ciki har da shugaban Kungiyar Yan Jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna  (NUJ), Kwamared Asma’u Yawo Halilu a babban taron da suka shirya yi a dakin taro na filin wasa na Ahmadu Bello ABS da ke Kaduna

Hakazalika, hukumar da ke kokarin rage hadurra ta kasa FRSC za ta kuma kaddamar da shirin a dukkanin sauran shiyyoyin Jihar wanda suka hada da Zariya da Kafanchan domin tabbatar da an samu cikakken hadin kai da wayar da kan al’umma da nufin samun ci gaba a Jihar.

Kwamanda Kabir Yusuf Nadabo, ya kuma kara jaddada kudurin hukumar na yin hadin gwiwa tare da sauran dukkanin hukumomi Jami’an tsaro na Jihar domin ganin sun gudanar da ayyukan su cikin nasara.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.