Related Articles
DAGA IMRANA ABDULLAHI
Honarabul Atiku Muhammad Yabo Sarkin Yabo, ya bayyana Gwamnan Jihar Sakkwato zababben Sanata Aminu Waziri Tambuwal a matsayin saukin shugaba mai kokari da aiki tukuru bisa niyyar al’umma ta ci gaba.
Honarabul Atiku Muhammad Yabo ya ce shi a matsayinsa na wanda ya san Sanata Aminu Waziri Tambuwal lokacin da yake Gwamnan Jihar manema labarai a garin Gusau ta Jihar Zamfara.
“Ina son shaidawa duniya da cewa idan har yan majalisar Dattawan Najeriya suka zabi Sanata Aminu Waziri Tambuwal a matsayin shugaban Dattawan Najeriya a majalisa ta Goma (10) tarayyar Najeriya za ta samu ci gaban da kowa zai yi alfahari da shi”.
Atiku Mohammad Yabo ya kara jaddada cewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal lokacin da yake Gwamnan Jihar Sakkwato aiwatar da ayyuka manya manya duk da nufin al’ummar Jihar su ci gaba.
” Sanata Tambuwal ya Gina makarantun da suka hada da Ajujuwan makarantun Firamare sama da dubu biyar da dari biyar (5500) a fadin Jihar Sakkwato ga kuma aikin shatalai talan titin Kwamnawa zuwa Shuni sai aikin Gadar tashar Illela da kuma aikin fadada titin gidaje 342 a Kasarawa.
Sai kuma aikin makarantar Yammata ta kimiyya da fasaha da kuma aikin filin wasanni na cikin daji mai daukar mutane dubu 14000 a Kasarawa da kuma aikin sabon titin bayan gari daga Kasarawa zuwa shuni
Sai kuma aikin ginin katafaren daki mai cin daruruwan Gadajen marasa lafiya a makarantun Foly da makarantun kiwon lafiya
Ga kuma aikin ginin ajujuwa a kowace Firamare a duk fadin Jihar Sakkwato, ha kuma aikin ginin cibiyoyin lafiya da suka kai sama da cibiyar lafiya 30 ga kuma aikin gyaran asibitoci tare da aikin ginin Masallatan juma’a 50 a Jihar, ga kuma aikin samar da motocin Bus – Bus ga makarantun Sakandare a duk fadin jihar Sakkwato baki daya.
Honarabul Atiku Muhammad Yabo Sarkin Yakin Yabo ya fayyacewa manema labarai a cikin mintuna Goma sha hudu da ya yi cewa zababben Sanata Aminu Waziri Tambuwal ayyukan da ya aiwatar a Jihar Sakkwato sai dai abin da mutum zai iya tunawa kawai wanda nan gaba zamu ci gaba da kawo maku si a cikin harshen Turanci da hausa.