Home / Labarai / Idan An Ba Noma Cikakkiyar Kulawa Za A Yaki Talauci, Yunwa, Yalwar Arziki A Samu Walwal Da Magance Matsalar Tsaro

Idan An Ba Noma Cikakkiyar Kulawa Za A Yaki Talauci, Yunwa, Yalwar Arziki A Samu Walwal Da Magance Matsalar Tsaro

Daga Bashir Bello, Majalisa Abuja.
Dan Majalisar Dattawa Mai wakiltar Mazabar Kwara ta Tsakiya a majalisar Dattawa da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, Sanata Mustapha Salihu, Shugaban Kwamitin Noma na Majalisar, a wani zama da suka yi na musamman ya yi  kira da a shirya da Ministocin Noma da Shugabannin Ma’aikatu  na Noma da ke Kasar.
Taron dai  ya gudana ne a Majalisar.
Sanata Mustapha ya ce idan aka ba Noma kulawar da ta dace za a yaki talauci da yunwa da rashin aikin yi da samun yalwatar arziki tare da magance barazanar tsaro da ta addabi kasarnan.
 Ya kara da cewa kamar yadda yake a cikin kudurin Majalisar Dinkin Duniya cewa duk kasar da ta ke so ta ci gaba to ya zama wajibi ta ware kaso 10 na kasafin kudin ta ga harkar Noma don wadata kasa da abinci.
“tun da aka kirkiri kasarnan tsohon Shugaban Kasa Marigayi Umaru Musa Yar’adua ne ya taba ware kaso 3 na kasafin Kudi na Kasar ga harkar Noma; saboda haka a wannan zamani da ake cikin tsananin talauci da matsi na tattalin arziki akwai bukatar a ware sama da kaso 10 ga harkar Noma”, inji  Sanata Mustapha.
Sanata Mustapha ya ce dalilin shirya taron na masu ruwa da tsaki na Noma na Gwamnatin Tarayya shi ne domin Majalisar ta ji da ga gare Su irin shirye-shirye da su ke da shi a kan harkar Noma domin a samu fahimta tsakanin Majalisar Dattawa da Su a wani mataki na wadata Kasa da abinci domin samun saukin rayuwa.
Ya ce Majalisar ta ji duk irin tsare-tsare da suke da shi a kan harkar Noma kuma Majalisar za ta yi duk mai yiwuwa wajen hada gwiwa da Fadar Shugaban Kasa domin ganin sun kasance a shafi guda a wani mataki na bawa Noma kulawar da ta dace don samar da abinci wadatacce wanda idan an yi hakan tabbas za a samu saukin rayuwa a kasarnan.
A jawabin  bangaren, Karamin Ministan Noma, Sanata Sabi Abdullahi wanda ya yiwa Yan Jaridu karin bayani gamai da taron ya ce manufar taron shine a samu fahimtar juna tsakanin Fadar Shugaban Kasa da Majalisar Taraiya a wani mataki na inganta harkar Noma wanda shine kashin bayan tattalin arzikin Najeriya.
Sanata Sabi ya kara da cewa a matsayin su na sababbin Ministoci da sababbin Yan Majalisar Taraiya akwai bukatar a sami fahimatar juna domin kauracewa rigingimu da ka iya aukuwa tsakanin Majalisar da Fadar Shugaban Kasa.
Ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya baiwa Noma mahimmanci saboda haka ne suke so a sami fahimtar juna don samar da wadaccen abinci wanda hakan zai kawo sauki ga Yan Najeriya musamman a wannan lokaci da ake fama da matsi na tattalin arziki.

About andiya

Check Also

The Daily Hug For Appreciation 2023

The daily hug for 28/11/23 is this appreciation of an echo shared by my dear …

Leave a Reply

Your email address will not be published.