Daga Imrana Abdullahi
Dokta Sulaiman Shuaibu Shinkafi, sanannen dan Gwagwarmaya ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Kasar Palasdinu da al’ummar Palasdinawa, inda ya kafa tutar kasar Palasdinu a gidansa da ke unguwar Badarawa cikin garin Kaduna da ke arewacin tarayyar Najeriya.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya kuma yi kira ga daukacin manyan kasashen duniya da suka hada da Najeriya da su taimakawa kasar Palasdinu da Palastinawa da addu’a su samu zaman lafiya da nufin Allah ta’ala ya yaye masu masifar da suke ciki.
#muna goyon bayan Palasdinawa🇵🇸