Daga Imrana Abdullahi
Rundunar yan Sandan Babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da kama wani shahararren mai Satar Jama’a mai suna Chinaza Philip, da ya addabi jama’ar yankin.
Kamar dai yadda wata takardar sanarwar da ya fito daga rundunar Yan Sandan babban birnin tarayya Abuja ta sanar mai dauke da sa hannun SP Josephine Adeh, mai magana da yawun rundunar a Abuja.
Sanarwar ta ce rundunar Yan Sanda ta kasa a Jihar Kaduna ce ta kama wannan Kasurgumin mai satar jama’a a ranar Alhamis 18 ga watan Janairu, 2024.
Kuma tuni aka mika wanda aka kama din a hannun jami’an rundunar Yan Sandan birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a 19 ga watan Janairu, 2024.
Zamu ci gaba da kawo maku bayanan a nan gaba….