Home / Big News / Jam’iyyar ADC Na Samun Gagarumar Nasara A Zamfara – Bashir Nafaru

Jam’iyyar ADC Na Samun Gagarumar Nasara A Zamfara – Bashir Nafaru

 

Daga Imrana Abdullahi
 Honarabul Bashir Nafaru, Sakataren Kudi na jam’iyyar ADC jihar Zamfara,ya bayyana cewa tafiyar jam’iyyar ADC a Jihar Zamfara na samun gagarumar Nasarar sakamakon wadansu shugabannin da suka shigo cikinta.
“Jam’iyyar ADC jam’iyyar ce mai alamar musabaha kuma jam’iyya ce mai son kawo sauyi a dukkan kasar Najeriya baki daya ba wai jihar Zamfara kawai ba sai dai za a ce jam’iyya ce ta talakawa domin talaka ya ji abin da yake ji a jikinsa a yanzu ya na son Samun saukin rayuwarsa, hakan ta sa za a ga mutane masu albarka na ta shigowa cikinta.
Nafaru ya kuma ci gaba da bayanin cewa sai wannan ya riko wancan ya riko domin Jam’iyya ce mai hada ka da nufin a samu kafa gwamnatin kasa da jihohi baki daya duk hakan da nufin samun gyaran kasa ne.
“Muna yin kira ga duk inda dan jam’iyyar ADC Yake da ya yi marhabin da ita domin a jihar Zamfara irin kungiyoyin Alhaji Atiku Abubakar Sale ruwan Dogara wa, Baraden Maru, akwai kuma kungiyoyi da za ta kai guda Goma a Jihar Zamfara kuma duk abin da suke fafutuka shi ne ya za su wayar da kan al’umma kowa ya fahimci meye ADC don haka ina kira ga daukacin ya’yan jam’iyya da ayi hakuri da juna a rike juna a kuma rike mutuncin juna muna yi wa Allah godiya domin abin da ya dace ADC ta fara mallaka tuni ta fara mallakar su tun daga matakin Mazabu zuwa matakin yan takarar Gwamna, Sanatoci, yan majalisar tarayya muna kira ga kowa ya fito ya nemi jama’a domin yanzu an shiga fagen neman jama’a hakan ta sa muke yin kira ga kowa duk mai sha’awar fitowa takara ya fito ya nuna lokaci ya yi ya nemi jama’a
Honarabul Bashir Nafaru, ya kuma yi gargadi ga dukkan ya’yan jam’iyyar masu takara da wadanda suke a matsayin mambobi mabiya da su hada kai a nemi mutane ba yin fada ba.

“Muna kuma kara godewa Allah da ya nuna mana cewa ADC ce jam’iyya ta biyu a Najeriya da yawan jama’a da karɓuwa a wajen kowa.
Nafaru, ya kuma lissafa wadansu shugabannin da ya ce jama’a na iya samun su a koda yaushe domin sune shugabanni a ADC, shugaban jam’iyya Kabiru Garba Uban Dawakin Tudun Wada Gusau, sai Sakataren tsare – tsare na kasa ma Alhaji Atiku Abubakar Sale Baraden Mary sai kuma Hajiya Ganiyat Kaura shugabar masu Gajeruwar rashin lafiya a jihar Zamfara don haka muna yi masu fatan alkairi kuma duk wanda ke son ya shiga cikin wannan tafiyar ya na iya tuntubar su

About andiya

Check Also

Bello Muhammad Zaki Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP zuwa ADC A Jigawa

    Daga Imrana Abdullahi Fitaccen Dan Jarida kuma Wanda ya yi wa tsohon Gwamnan …

Leave a Reply

Your email address will not be published.