Home / Labarai / Jaridar Shield online Ta Karrama Adamu Mohammad Gidado Gishirin Ma’aurata

Jaridar Shield online Ta Karrama Adamu Mohammad Gidado Gishirin Ma’aurata

Jaridar Shield online Ta Karrama Adamu Mohammad Gidado Gishirin Ma’aurata
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin jaridar shield da Garkuwa da ake wallafawa a yanar Gizo a Turanci da hausa da kuma a takarda da suke aikin binciko ainihin mutanen da suka yi fice wajen inganta rayuwar al’umma ko dai ta fuskar Koyar da sana’o’i, Noma da Kiwo ta yadda za a samu mutanen da Nijeriya, nahiyar Afrika da kasa baki daya za su yi alfahari da su.
Hakan ya sa wannan jaridar da ta yi nisa wajen yin bincike a fannonin al’amura daban daban ta fitar da babbar cibiyar da ta yi fice wajen koyawa Maza da Mata sana’o’i da kuma harkar Noma da Kiwo ta Gishirin Ma’aurata Skills Aquisition Centre” da ke da katafaren Ofis a cikin garin Kaduna, inda aka Karrama shugaban wannan cibiya Alhaji Adamu Muhammd Gudado da ake yi wa lakabi da mai gishiri  da kuma ita cibiyar kanta da nufin sanar da jama’a wasu su yi ko yi da abin da cibiyar ke aiwatarwa.
Hakika tunani da kuma aikin da cibiyar nan take aiwatarwa lamari ne za a ce ana yinsa ne da nufin sauta al’umma su san inda aka dosa sannan kowa ya dogara da kansa.
Mace ba za ta samu matsalar babu ba idan ta iya sana’a shi kuma Namiji zai samu abin dogaro da kansa ya tallafa wa wanda yakamata.
Ita dai cibiyar Gishirin Ma’aurata ta dade ta na aiwatar da aikin horar da jama’a harkoki irin na fadakarwa yadda za a samu rance daga wurin Gwamnatin tarayya musamman a babban  Bankin Nijeriya da dai sauran ayyukan dogaro da kai.
Ko a kwanan nan sai da wannan cibiyar ta horar da mata da maza irin yadda ake kiwon Kifi da kuma Kaji, shi dai wannan shirin an yi shi ne tare da hadin Gwiwar cibiyar Sanata Uba Sani da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna kamar yadda aka bayyana a wajen wani taron da ya gudana a Kaduna domin mikawa duk wadanda suka samu horon takardar shaidar sun halarci horon da kuma ba su kajin da Kifin da za su kafa kiwon da su.
Mutane dubu daya (1000 ) dai ake kokarin horaswa karkashin shirin.
Wannan karramawa da jaridar theshieldg.com ta yanar Gizo da kuma wallafa wa takarda sun yanke shawarar a mika wannan karramawar ne ga shugaban cibiyar Gishirin Ma’aurata ta yadda zai samu kwarin Gwiwar cibiya da aikin da yake yi ganin cewa mutane na kallon abin da yake yi, dimbin jama’a na amfana.
Kuma nan gaba za mu Sanya bidiyon wannan a shafin youtube mai adireshi kamar haka blueinknews da kuma the shield da Garkuwa duk a yutub domin a kalli bidiyon yadda bikin ya gudana musamman irin yadda ake mika wa wadanda aka horar Kaji da Kifin da za su kiwata.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.