Jihar Bauchi ta kammala shirye-shiryen rabon ruwan zamzam ga maniyyatan da suka kammala aikin Hajjin daga ranar Laraba 20 ga Satumba, 2023.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da hukumar jin dadin alhazai ta jihar Bauchi ta fitar kan shirin raba ruwan zamzam ga mahajjatan jihar a shekarar 2023.
Sanarwar ta bayyana cewa jihar Bauchi ta samu adadin zamzam da aka shirya domin rabawa.
Haka kuma an bukaci Alhazai na Hukumar da Alhazai da Gwamnati ta dauki nauyin shirin da tsarin tanadin aikin Hajji da su zo hedikwatar Hukumar tun daga ranar da aka tsara za su karbi ruwan Zam Zam din su yayin da Alhazan da suke daga matakin Karamar Hukumar za su tunkari Jami’an Hukumar Alhazai na Karamar Hukumar.
Sanarwar ta kuma kara da cewa ana sa ran dukkan maniyyatan za su gabatar da Fasfunansu (E-passport)da kuma kwafin bayanansa a wurin karbar Zam Zam din.
Daga Jamilu Barau