Home / Uncategorized / Jihar Kogi Za Ta Zamo Gagarabadau Wajen Fitar Da Kayan Noma Kasashen Waje – Isma’il Isa

Jihar Kogi Za Ta Zamo Gagarabadau Wajen Fitar Da Kayan Noma Kasashen Waje – Isma’il Isa

Daga Imrana Abdullah
  An bayyana batun samar da Inshorar lafiya ga dukkan yan fansho a jihar Kogi a matsayin abin a ya ba kasancewar taimako ne da aka yi wa dukkan yan fansho kyauta domin kula da lafiyarsu bayan ajiye kammala aiki.
Mai ba gwamnan jihar Kogi shawara a kan hulda da kafafen yada labarai Malam Isma’il Isa, ya shaidawa Manama labarai hakan a Kaduna, inda ya ce a can baya tsarin kula da lafiyar ba kowa ne dan fansho ba ne  ke amfana da shi ba amma zuwan wannan gwamnatin ya zama kowa duk na amfana.
A game da batun samar da ma’aikatar kula da masu kiwon dabbobi kuwa sai Malam Isma’ila Isa ya ce kamar yadda kowa ya sani ne Jihar Kogi tamkar wata karamar Najeriya ce domin mafi akasarin wadansu abubuwa da ke faruwa a Jihar Legas na faruwa kuma a Jihar Kogi wannan ne ma ya sa aka samar da wannan ma’aikata domin samun amfani duk wani abu da ke haifar wa kasa da jama’arta ci gaba musamman a bajgaren Dabbobi.
Kuma hakan ta sa aka ajiye wani babban aiki kula da al’amuran Dabbobi karkashin tsarin L- press aka ajiye shi a kusa  da makarantar kimiyya da fasaha da ke Osara, da aka samar da babbar Gona mai yawan hekta dari biyu zuwa dari Uku domin yin aikin gwaji kuma akwai wani ingantaccen tsarin da aka yi domin yin aiki tare tsakanin masu Noma da masu kiwon dabbobi wanda ba za a samu wata matsala ba kamar can a baya da ake samun matsala tsakanin Juna.
” Akwai wani taarin da ma’aikatar kula da kiwon dabbobi take da shi na ganin an yi  wa dukkan masu kiwon dabbobi rajista ta yadda za a samar da babban kundin rajistar masu kiwon dabbobi a Jihar koda mutum mai kiwon dabbobi zai tashi daga wancan wuri zuwa wancan za a iya sanin inda ya nufa duk wannan kokari ne na ganin ba a samu matsalar tashe tashen hankalin da ake fama da shi a can baya ba tsakanin Manoma da makiyaya duk muna son yin maganin faruwar hakan a jihar Kogi”.
Akwai wani tsarin da muke kokarin yi a wannan shekarar inda aka samar da babban fili mai fadin hekta 240 da za a sanya Manoma da Makiyaya wuri daya da kowa zai yi aikinsa kamar yadda ya dace
“Zan yi amfani da wannan damar in sanar da cewa tsakanin watan Yuni na shekarar da ta galata da watan Satumba ko Disamba  jihar Kogi ta kasance wadda ke fama da hauhawar farashin kayan abinci amma a halin yanzu duk ba wannan komai ya dawo kasa kwarai farashi ya sauka misali idan aka  mudun gari a wancan lokacin da na ambata da mudin gari ke kaiwa dubu hudu a yanzu ya sauka domin ana samu dubu biyu kun ga sauki ya samu kwarai hakan ya sanya a yanzu ake ta koakrin kara ingantawa da habbaka Noma a Jihar Kogi ta yadda jihar za ta zama wadda ta fi kowace Jiha fitar da abinci zuwa kasashen Dunipace.

About andiya

Check Also

GOC task parents on proper upbringing of children, community service

  Maj. Gen. Ibikunle Ajose, the General Officer Commanding (GOC) 8 Division of Nigerian Army …

Leave a Reply

Your email address will not be published.