Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada wa duniya cewa Jihar Zamfara na da babbar damar bunƙasa harkokin noma, yana mai cewa noma ne ginshiƙin ci gaban tattalin arzikin jihar da Arewa maso Yamma gaba ɗaya.
Gwamna Lawal ya yi wannan bayani ne yayin da ya halarci Babban Taron Masu Zuba Jari na Afirka (AIF), Ranakun Kasuwar Zuba Jari na 2025 da aka gudanar daga ranakun 26 zuwa 28 ga watan Nuwamba, 2025, a birnin Rabat da ke ƙasar Morocco.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce taron ya haɗa manyan masu zuba jari daga sassa daban-daban na Afirka, inda aka tattauna manyan yarjejeniyoyin kasuwanci tare da lalabo hanyoyin aiwatar da ainihin zuba jari a faɗin nahiyar.
Sanarwar ta ce, taron, wanda Bankin Raya Afirka tare da haɗin gwiwar wasu manyan cibiyoyi guda shida ke jagoranta, ya mayar da Taron Zuba Jari na Afrika a matsayin dandali na musamman da ke hanzarta tsara manyan ayyukan ci gaba da tara kuɗaɗen da za su tafiyar da su a Afirka.
A yayin taron, Gwamna Lawal ya halarci manyan tattaunawa kan yadda za a bunƙasa zuba jarin kamfanoni masu zaman kansu ta hanyar samar da yanayi mai sauƙi, da kuma zaman muhawara kan faɗaɗa zuba jari ta tsarin haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu, tare da tattaunawa kan yadda za a tara jarin cikin gida domin ingiza ci gaban Afirka.
A gefe guda kuma, Gwamnan ya rattaba hannu kan wata muhimmiya Yarjejeniyar Fahimtar Juna tsakanin Gwamnatin Jihar Zamfara da Hukumar ‘Ministry of Finance Incorporated’ (MOFI) domin haɓaka gagarumin shirin sauya fasalin noma a jihar.

Yarjejeniyar ta sanya Zamfara a cikin jihohin da za su fi cin gajiyar shirin INTEGRANIUM na ƙasa, wanda ke mai da hankali kan noma na zamani, sarrafa amfanin gona, hanyoyin adana bayan girbi da kuma buɗe hanyoyin fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin duniya.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, Gwamnatin Jihar Zamfara za ta samar da filaye, ababen more rayuwa, tsaro da manufofi masu sauƙi, yayin da MOFI za ta jagoranci samo kuɗaɗen zuba jari, jawo hankalin masu zuba jari, da tallafa wa aiwatar da manyan ayyukan noma.
Ana sa ran wannan haɗin gwiwar zai samar da dubban ayyukan yi, ya ƙara wadatar abinci, ya ƙarfafa darajar amfanin gona tare da hanzarta ci gaban tattalin arziki mai shafar talakawa a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya.

Da yake jawabi ga masu zuba jari a wani zagayen tattaunawa, Gwamna Lawal ya bayyana Zamfara a matsayin cibiyar noma ta haƙiƙa, yana mai cewa gwamnatinsa na samun gagarumar nasara a fannoni daban-daban.
A cewarsa, “Ina matuƙar farin ciki da ganin Bankin Raya Afirka tare da sauran manyan masu zuba jari na duniya sun halarci wannan taro. Noma ne gaba ga Afirka, Nijeriya da kuma Zamfara musamman, saboda yalwar damar da ake da ita. A Zamfara, noma shi ne rinjayenmu. Muna noman kusan dukkan nau’o’in amfanin gona; ba mu tsaya kan wake ko waken soya kaɗai ba. Muna da yalwatacciyar ƙasa mai albarka.

“Ina gayyatar dukkan masu zuba jari na duniya su zo Zamfara. A halin yanzu muna matakin ƙarshe na kammala filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na jigilar kaya, muna gina otel mai matsayi na biyar, tare da manyan ayyukan sabunta birane a faɗin jihar.”
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa na ɗora babban alheri kan noma a matsayin ginshiƙin wanzar da ayyukan yi ga matasa, rage talauci da tabbatar da tsaron abinci mai ɗorewa a Zamfara.
THESHIELD Garkuwa