Home / Labarai / JIRGIN KADUNA ZUWA ABUJA YA YI HADARI

JIRGIN KADUNA ZUWA ABUJA YA YI HADARI

Bayanan da muke samu daga wajen wasu fasinjojin Jirgin kasa da ke Jigila saga garin Kaduna zuwa Abuja ya yi hadari da misalin karfe daya da wasu mintoci na ranar yau Juma’a.

Kamar yadda muka samu labari daga wasu fasinjojin da suke cikin Jirgin daga garin Kaduna zuwa Tashar Kubwa a Abuja, sun ce da misalin karfe daya da yan mintuna ne kusan saura mintuna biyu Jirgin ya kai tashar da za su sauka domin har an yi masu sanarwa a cikin Jirgin cewa kowa ya shirya mai kaya ya hada kayansa wanda ya cure takalmi ya Sanya abinsa domin an kusa sauka, sai kawai suka ji Jirgin kamar ya taka Burki nan da nan wadanda suka tashi tsaye suna kusa da hanyar ficewa sai suka kusa faduwa har sai da suka rirrike wasu karafuna na Jirgin domin kada su fadi daga nan ne suka gane cewa ba birki bane.

Sai aka sanar da su cewa Jirgin ne ya yi hadari ya saki hanyarsa, amma dai ba a samu salwantar rai ba kamar yadda majiyar ta shaida mana.

Nan da nan sai aka Sanya wa fasinjoji wata kujera wasu na takawa suna fitowa wasu kuma na kanawa su yi tsalle su fice haka dai har suna fita cikin Jirgin suka rika takawa a kasa domin su karasa ainihin inda yakamata, wannan ne abin da ya faru da fasinjojin Jirgin a yau Juma’a muna kuma jira mu samu karin bayani nan gaba tukunna.

About andiya

Check Also

Sokoto APC supporters take over major streets for Aliyu Sokoto’s victory

  By Suleiman Adamu, Sokoto   It has been jubilation all through by thousands of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.