Home / Big News / Kalaman Shugaban Amurka Bori Ne Ke Neman Kashe Boka – Kailani Muhammad

Kalaman Shugaban Amurka Bori Ne Ke Neman Kashe Boka – Kailani Muhammad

Kungiyar da ta Kira kanta masu kishin Najeriya karkashin jagirancin Farfesa Kailani Muhammad ta bayyana batun zancen shugaban Amurka Donald Trump da cewa bori ne ke Neman kashe Boka domin matsalar Najeriya ta masu Mulki ne BA wata magana.
Farfesa Kailani ya dai bayyana hakan ne a wajen wani Babban Taron Manema labarai da ya Kira a Kaduna.
Sai kuma kamar yadda ya ce sai Malamai da suka Zama Yan cika bakinka Kai Gum.
“Wannan taron Manema labarai ne a Kan irin abubuwan da suka faru a Yan kwanaki nan da shugaban Amurka ya ce sai kawo WA Najeriya Hari Wanda nan da nan cikin shugabannin mu ya duri ruwa domin lamarin ya na su mamamki Wanda ya Fara magana Shi ne Sanata Ali Ndume da ya yi magana ya ce Amurka BA ta yi adalci na yanzu takardar izinin Shiga Amurka ma an ce BA za a Bari suje Amurka BA sanan kudin Yan Najeriya da aka ajiye a can za a Sanya takunkumi a Kai sannan za a kawo mana hari sannan kuma hidajensu da ke can Amurka duk ita Amurka za ta rike abin kuma sai ya zo duk kasa ta dauka, inda muka ga Sama’ila Kawu yazo Kaduna a satin da ya gabata aka Tara sarakuna da Yan jama’atunnasarul Islam da malamai da Yan Siyasa aka ce akwai jihohi 12 da suke yin Shari’a za a Fara da su za a kawo Hari Shi yasa aka yi taro aka yadda za a je a ga Trump.
” sai na CE ai sun yi latti domin ina suke lokacin da su Kuka suka yi ta yin rubutu suka je Amurka sai muka kalubalance su muka ce Kai Dan Najeriya ne kuma kana daular Musulunci ne a Sakkwato BA a tsangwameka BA kuma BA Wanda ya yi rubutu daga bangaren musulmi cewa wannan maganar karya CE babu sam, aka zo kungiyar CAN ta yi rubutu aka je majalisar dattawa ta Amurka suka Gaya masu kabli da ba’adi BA Wanda ya bi cikin su Malamai da ke kwambo su Sanya hula a nan suna yin wa’azi ai ni na daina Jin wa’azinsu ma a yanzu domin BA amfani, sannan Yan Siyasa in Ban da cin amana BA abin da suka yasa a gaba Amma GA talakawa kowa na Kuka wani ya zo abinci da zai ci na Rana ma babu Shi duk da Allah ya wadatar da kasar an ce BA abin da BA mu da shi na arzikin kasa.
“Amma rashin tsoron Allah, rashin gaskiya da yaudara duk da Allah ya ce Kada mu yi. Wasu sun yarda ne kawai Amma Bai Kai zuciyarsu BA, Amma saboda me mutum zai rika Tara makudan kudin da Bai San su BA kwallin duniya kawai dai wadatar zuci Allah ya Baka Kudi Ka ci Ka Sha Ka yi addininka kafin Allah ya karbi rayuwarka, sai an Gina gidaje gashi nan turawan sun kwace. Amma Ku shugabanni a tsawon shekaru 48 da suka Gabatar BA abin da kuka tsinana in kuma akwai abin da aka zinana azo a Gaya mana domin duk Shi ya kawo wannan da rarrabuwar Kai muna da abokai da suka kasance kiristoci tun da na Fara yin karatun difiloma a Legas tare muke da Yan Kaduna ta Kudu har ma da wadanda BA su ma yarda akwai Allah BA don haka muna fatan za su Gyara su SA Allah a gaba su daina haifar da matsala da Tara kudin da in an Tara su idan mutum ya mutu Yan ma BA su iya zuwa su CE a BA su kudin duk an rike baka iya zuwa Ka samu kudin BA.
Don haka su Gyara su SA Allah a gaba a tausayawa talakawan kasa kuma BA lokacin ne na zage zage BA a dawo a Gyara kawai mu so juna daga nana duniya har lahira Kada fa a Bari sai talakawan kasa sun yi masu bore don idan tura ta Kai mutum bango yau Bai ci BA gobe BA a ci BA sai ya yanke hukuncin komai ta Ka Zama ta Zama, sai a Gyara duk kudin da suka sace suka ajiye a cikin gidajen su a fito da su a Fara rarraba kudin ya Kai GA talaka.
Ayi riko da ayar alkur’ani da ta ce ya rasulullah Ka Gaya WA yayan annabi Adama Alkur’ani BA warka BA CE BA Tatsuniya BA CE shiriya CE daga Allah, don haka idan mutum na ganin ya samo wani Abu ya haye KO KO kuma ma rashin alkiyamar ma BA zai zo BA to, sune suka kafirta, Allah ya amince mana ayi aiki da gaskiya daadalci a so Yan kasa aso juna.

About andiya

Check Also

Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861 Ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.