Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
….Mutane Su dai kara hakuri domin ci gaba da ingantuwar tattalin arzikin kasa na zuwa
Hajiya Fatima Wali Abdurrahman, babbar jami’ace a kamfanin Dangote ta bayyana kamfanin a matsayin wanda ya fi kowa samar da dimbin ayyukan yi ga jama’a, wanda hakan ya faru ne sakamakon irin kokari da jajircewar Alhaji Aliko Dangote da ya kasance babban jigo a duk nahiyar Afirka baki daya.
Hajiya Fatima Wali, ta bayyana hakan ne a wajen bikin ranar kamfanin Dangote da aka yi a kasuwar duniyar kasa da kasa da ke ci yanzu haka a Kaduna karo na 45.
Hajiya Fatima ta kuma ja hankalin jama’a a game da bukatar da ake da ita na kowa ya kara hakuri a game da batun kara inganta tattalin arzikin kasa da ake ciki a halin yanzu.
Inda ta bayyana lamarin ga manema labarai da cewa kamar ” mace ce mai yin nakudar haihuwa, hakika nakudar haihuwa akwai zafi amma bayan an haihu kuma sai murna da farin ciki, saboda haka lamarin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu abu ne da ke bukatar a kara hakuri domin nan gaba kadan komai zai inganta a ci gaba da murna da farin ciki da ikon Allah”.
Fatima, ta kuma bayyana Alhaji Aliko Dangite a matsayin cikakken dan kishin kasa da ke da kishin Najeriya,Afirka da duniya baki daya sakamakon kokarinsa na inganta harkokin rayuwar jama’ar kasa baki daya.
Ta ci gaba da bayanin cewa hakika taken kasuwar na Bana yazo dai dai da irin kudiri da kuma dimbin hasashe da aiki a aikace na shugaban kamfanin rukunin kamfanonin Dangote na sarrafa irin albarkatun da muke da su a cikin Najeriya, domin yin amfani ko sarrafa albarkatun kasa da muke da su a Najeriya zai kara bunkasa tattalin arzikin da muke da shi ta yadda za mu yi gogayya da duniya.
Fatima ta ce ” batun karuwar hauhawar farashin kaya duk wannan su a kamfanin Dangote ba su san da shi ba domin basa kara farashin kayansu a kullum, kuma shi kamfanin Dangote baya sayar da kayansa ga masu yin amfani da shi da kwara kwara sai diloli masu sayan motoci tireloli da yawa don haka ba su ne da alhakin kara fara shi a kullum kullum ba”.
“Ya dace jama’a su Sani cewa Alhaji Aliko Dangote shugaban rukunin kamfanonin Dangote ya daukarwa kansa batun kudin Dakon kayansa, misali abin da wanda ya sayi kayansa na Siminti a Jihar Banuwai kudin da za a biya dai dai yake da kudin da wanda ya sayi kayan za a kai masa Jihar Borno, lallai Aliko Dangote, ya daukarwa kansa wannan domin jama’ar kasa kowa ya amfana”.
“Alhaji Aliko Dangote na matukar Kaunar ganin Najeriya da Afirka baki daya sun ci gaba saboda haka ne ma duk yake kokari da mayar da himma a koda yaushe domin ganin kwalliya ta biya kudin Sabulu a koda yaushe”.
Hajiya Fatima Wali, ta kara da cewa kamfanin Dangote na halartar kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna tsawon shekaru Talatin (30) kenan.Kasuwar duniya ta Kaduna na da matukar muhimmanci a gare mu domin Kaduna ce hedikwatar siyasar arewacin Najeriya.
“Muna kuma yin aikin hadin Gwiwa da Gwamnati tare da mutanen jihar Kaduna a fannoni daban daban, duk da nufin karfafa zumunci da kokarin bunkasa tattalin arzikin kasa”.
Saboda haka in ma za a yi tarihin kasar nan hakika dole ne a yi wa kamfanin Dangote adalci kuma musamman ma Alhaji Aliko Dangote”.
“Masana’antun mu, daga na Siminti zuwa Sukari kuma daga na Gishiri zuwa na Aikin Noma da sauransu, da kuma na kwanan nan na Mai da Iskar Gas duk an yi su ne da nufin bunkasa irin ma’adanan da ake samu a cikin gida wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da kara samun kudin shiga a kasa baki daya.
Kuma ko a fannin batun taimakawa al’umma ma ba a barmu a baya ba, domin muna ci gaba da taimakawa al’umma da Gwamnatin Jihar Kaduna da kasa baki daya, ta hanyar ayyukan gidauniyar Aliko Dangote
“A halin yanzu kamfanin Dangote ya zama abin misali ta yadda za a samu damar abin da ake da shi a cikin kasa ayi amfani da shi a Farfado da tattalin arziki mai dorewa”.
Hajiya Fatima Wali, ta yi kira ga daukacin jama’a da su kara hada kai da yin aiki tukuru ta yadda za a samu masana’antu na cikin gida su kara bunkasa da haka ne nake cewa ya dace kowa ya yi koyi da irin Namijin kokarin Dangote domin kara inganta al’amura a kasa baki daya.
Muna kuma taya daukacin mambobin da ke shirya wannan kasuwa ta KADCCIMA da Gwamnatin Jihar Kaduna tare da jama’ar Jihar murnar samun damar shirya kasuwar baje koli a wannan shekarar.
Muna kuma gayyatar kowa da kowa da ya ziyarci rumfar mu da ke cikin wannan kasuwar domin ganewa idanunsa irin abubuwan da muke yi a kamfanin Dangote.