.Daga Imrana Abdullahi
Rukunin kamfanonin NASCON Plc, da aka fi sani da Gishirin Dangote, sun bayar da gagarumar kyauta ga manyan kwastomominsa guda Hamsin kyautar biliyoyin Kudi Da Manyan Motocin Daukar Kaya duk saboda irin kokarin da suke yi na ganin kayan sun samu karɓuwa ga al’umma.
An dai karrama wadanda suka samu nasarar samun wannan kyautar ne wajen wani gagarumin taron cin abincin Dare da aka shirya na shekarar 2025, a Abuja, wanda ya samu halartar babban jagora Da ke kan gaba a nahiyar Afirka a kan harkokin kamfanoni da masana’antu wanda ya kasance shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote tare da mataimakinsa Olakunle Ake.
Kamfanin “NASCON Allied Industries Plc, daya ne daga cikin rukunin kamfanonin “Dangote Industries Limited”, kuma sune masu samar da ingantaccen Gishiri da kuma kayan dandanon abinci na Dangote.
Da yake jawabi a wajen taron Aliko Dangote ya kara jadda cewa irin wannan babban taron bayar da kyauta ga kwastomomi wata alama ce da ke nuni da cewa kamfanin ya san muhimmancin irin hulda da ke tsakaninsu kuma hakan zai kara tabbatar da hasashen da ake da shi na ganin an samar da ingantattun kayayyakin da duniya za ta ci gaba da yin alfahari da su.
Ya kuma jinjinawa jagorori da ma’aikatan kamfanin bisa juriya da kwazo aikin da suke nunawa musamman ta fuskar kwarewar aiki wanda hakan ya sa aka samu kyakkyawar dangantaka tsakanin dukkan masu hulda da kamfanin.
Da yake tofa albarkacin bakinsa mataimakin shugaban rukunin Kamfanonin Dangote Olakunle Ake,wanda kuma shi ne shugaban majalisar koli na kamfanin NASCON, bayyana ainihin kwastomomin ya yi da cewa wata kadara ce mai muhimmanci. Inda ya ce wannan taron bayar da kyauta ga manyan kwastomomin alama ce ta kyakkyawar dangantaka da ke nuni da cewa ba za a taba samun ci gaba ba in har ba a yi aiki tare da.
Haka ita ma sabuwar babbar Daraktan kamfanin matatar man fetur ta Dangote, godiya ta yi ga kwastomomi bisa irin yadda suke yin hulda tare da gaskiya da amana, abin da ya bayyana da cewa hakan ne kashin bayan ci gaban kamfanin baki daya.
Haka ita ma a nata jawabin Mariya Aliko Dangote, daraktar da ke kula da harkokin Kasuwanci Na Kamfanin Siminti da abinci, cewa ta yi hakika samun ingantacciyar nasara na samuwa ne ta irin yadda ake samun kyakkyawar alaka tsakanin kamfani da masu yin hulɗar sayen kayansa don haka ne ci gaban da kamfani zai samu shi ne ya hanyar taimako daga Kwastomominsa.
Shiko Manajan Daraktan kamfanin NASCON, Aderemi Saka, cewa ya yi wannan babban taron liyafar cin abincin dare an shirya shi ne domin a bayyana irin farin ciki da murna ga kwastomomi domin samun nasarar kamfanin ya dogara ne ga irin kokarinsu har su rika sayen kayan kamfanin.
Da yake jawabi a madadin wadanda aka ba kyautar Ali Balarabe,da ya samu mota mai daukar Tan ashirin (20) na kaya da kuma lamunin Kudi, godiya ya yi ga kamfanin da har aka zakulo shi don haka ne ya ce zai ci gaba da yin hulda da kamfanin bilhakki da gaskiya.
Sauran da suka samu nasarar karbar wannan kyautar sun hada da Alhaji Ibrahim Shida, Muabsa Integrated Services, Fanisau Enterprises,Idris Saleh Nigeria Limited,Sani Adamu Trader, GIA Global Concept.
THESHIELD Garkuwa